Zaɓen Osun: ‘Yan sanda sun magantu kan zargin mamaye gidan kakakin majalisar dokokin jihar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda ta sanar da cewa ba ta tabbatar da zargin da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Osun, Adewale Egbedun ya yi ba na cewa wasu mutane masu ɗamara sun mamaye gidansa a safiyar ranar Asabar yayin da masu zaɓe ke shirin kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar da ke gudana.

Wannan zargi ya haifar da fargaba kan halin tsaro acikin al’ummar jihar a safiyar zaɓen, inda aka samu wasu rahotanni da suka ce kakakin ya koka da misalin karfe 6 na safe wajen yin iƙirarin wasu mutane masu ɗamara sun kewaye gidansa.

Saidai kakakin rundunar ‘yan sanda, Anietie Iniedu ya ce sun amsa wa ƙorafin, amma ba su tabbatar ko hakan ya faru ba a gidan kakakin. A cewarsa, an tura jami’an ‘yan sanda zuwa yankin bayan samun rahoton tare da umartar DPOn ‘yan sandan yankin da ya je wajen domin gane wa idanunsa.

Ya bayyana cewa, jami’an sun kasa tabbatar da zargin bayan cika umarnin da rundunar da ta yi musu na zuwa yankin domin gano haƙiƙanin al’amarin.

Ya ƙara da cewa, kasancewar rundunar ta ɗauki al’amarin da girma ya sa ta tura jami’ai zuwa wurin don tabbatar da cika ƙa’idojin aikinta.

A wani ɓangare, rundunar ta ce jami’an nata sun yi nasarar cafke wasu mutane guda 300 a gidan wani ɗan siyasar Osun yayin watsi da iƙirarin mamayar kakakin jihar. Saidai ba ta bayyana ko hakan na da alaƙa da zargin Egbedun ba ko akasin haka.

By Babaji