Babban ɗan Ganduje ya koma APC bayan watanni uku da shiga NDC ta Kwankwaso

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Abdulaziz Umar Ganduje, wato ɗan tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya koma jam’iyyar bayan ficewa daga NDC.

Abdulaziz ya koma APC a hukumance ne a Gundumarsa ta Ganduje da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a ranar Lahadi, inda ya karɓi katinsa na zama mamba. An ga yadda wasu jami’an jam’iyya da magoya baya suka halarci wajen sauya sheƙar, matakin da ake gani a matsayin jaddada biyayyarsa ga tsarin APC a Kano.

Da fari Abdulaziz ya shiga jam’iyyar NDC tare da yankar tikitin shiga takarar kujerar ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado.

A baya dai an yi ta tsokaci akan matakin nasa na shiga tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda sun jima suna hamayyar siyasa da mahaifinsa.

Komawarsa APC na zuwa ne bayan bayan an rufe karɓar sunayen ‘yan takara, wanda hakan ke nuna matakin nasa ya ɗauki wani salo a madadin cimma muradin zaɓe.

By Babaji

Leave a Reply