2027: Atiku da ADC na shirin gyara ƙorafin ƙalubalantar cancantar shigar Tinubu zaɓen

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ɗage sauraron ƙorafin da ke neman a yi kwaskwarima ga ƙarar da su tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar da jam’iyyar ADC suka shigar akan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jam’iyyar APC da Hukumar Zaɓe Ƙasa (INEC).

A zamanta na ranar Litinin ƙarƙashin Mai Sha’ir Inyang Ekwo, kotun ta ce ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2026. An gabatar da ƙorafin mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026 ne ga Mai Shari’a Ekwo.

A yayin jawabinsa, lauyan da ke kare ɓangaren masu ƙara, Joseph Silas ya shaida wa kotun cewa an riga da an damƙa wa baki ɗaya ɓangarorin masu kare ƙara ƙorafin a hukumance kuma a lokacin da aka tsara, sannan su kuma sun bayar da amsa a kai.

Cif Wole Olanipekun (SAN), wanda shi ne lauya mai kare Shugaba Tinubu, ya ce a zaman da kotu ta yi a baya a ranar 1 ga Satumba, an ba wa lauyan da ke kare APC, Popoola Owosanya damar karɓar bayanan kotu a madadin mutum na farko da ake ƙara.

Saidai Olanipekun ya faɗa wa kotun cewa lauyan masu ƙarar da ya nemi kotun ta bayar da izinin aike wa Tinubu ƙorafin ya yi watsi da buƙatar haka, yana mai zargin ɓangaren masu ƙara da yunƙurin “yaudarar kotun” ta hanyar iƙirarin cewa ba su samu damar aike wa shugaban ƙorafin ba.

Silas ya kuma shaida wa kotun batun shirin masu ƙarar na yin gyara ga bayanan farko da suka gabatar, yana mai cewa an sanar da masu kare ƙara al’amarin. Daga nan ne alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 13 ga Oktoba, 2026.

By Babaji

Leave a Reply