‎UNC ta wayar da kai kan zaman lafiya da yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‎
‎Ƙungiyar United Nigerian Chaplaincy (UNC), Katsina Command, ta gudanar da taron wayar da kan al’umma kan muhimmancin zaman lafiya da illolin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a shiyyar Daura.
‎
‎An gudanar da taron ne a sakatariyar ƙaramar hukumar Daura, a matsayin wani ɓangare na rangadin wayar da kai da ƙungiyar ke gudanarwa a shiyyoyi uku na Jihar Katsina.
‎
‎A yayin taron, mahalarta sun tattauna kan yadda shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ke taimakawa wajen haifar da matsalolin tsaro da sauran munanan halaye, musamman tsakanin matasa.
‎
‎An kuma yi kira ga al’umma da su ƙara ba da haɗin kai ga gwamnati da hukumomin tsaro wajen daƙile yaɗuwar miyagun ƙwayoyi da sauran abubuwan da ke barazana ga zaman lafiya.
‎
‎Haka kuma, an yi kira na musamman ga matasa da su guji shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, tare da mayar da hankali kan ilimi, sana’o’i da sauran abubuwan da za su taimaka wajen gina kyakkyawar makoma.

Darakta na ƙasa, Muslim Affairs na UNC, Sheikh Dr. Isma’il, na daga cikin waɗanda suka jagoranci taron, tare da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
‎
‎Shugaban ƙaramar hukumar Daura, Hon. Bala Musa Daura, ya jaddada goyon bayansa ga shirin ƙungiyar, musamman ƙoƙarinta na inganta zaman lafiya tsakanin al’ummomin addinai daban-daban.
‎
‎Kwamandan UNC na Jihar Katsina, Bello Isah, ya bayyana cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin addini da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da yaƙi da matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
‎
‎Ya kuma yi kira ga matasa da su “farka” su fahimci illolin miyagun ƙwayoyi, tare da rungumar ilimi da sana’o’i domin gina makoma mai kyau da zaman lafiya a cikin al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply