
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya sallami Rashida Adamu, wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa’a daga muƙaminta na mai taimakawa ta musamman a ofishinsa.
Hakan na ƙunshe ne a wata takarda da mai taimaka wa sanatan akan hulɗa da jama’a, Shitu Madaki Ƙunchi ya fitar a ranar Litinin, 28 ga Satumba.
A kwanan baya ne dai Sanata Barau ya sallami ɗaya daga cikin masu mataimaka masa, Umar Alhassan, wanda aka fi sani da King Indara bayan wata wallafa da ya yi a Soshiyal Mediya da ke sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano.
A cewar sanarwar, matakin na yanzu ya biyo bayan wasu zarge-zarge ne da Rashida ta yi akan magoya baya, zagon-ƙasa ga jam’iyyar APC da kuma wasu kalaman suka akan Sanata Barau.
An fitar da sanarwar ne bayan zargin cewa akwai masu yunƙurin lalata siyasar mataimakin shugaban majalisar a Jihar Kano da kuma cikin APC, waɗanda a baya an bai wa wasu muƙamai daga cikinsu ta hannunsa.
