SSS ta janye shirin dakatar da cigaba da shari’ar Sowore ta ɓatanci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Lauyan da ya gabatar da tuhuma kan Ɗan gwagwarmaya kuma mawallafin ShaharaReporters ta bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin “babban ɓarawo”, ya musanta samun bayanin wani shirin Hukumar Tsaro ta Farin (SSS) na dakatar da shari’ar har sai bayan zaɓen 2027.

Lauyan, Akinlolu Kehinde (SAN), ya musanta haka ne a ranar Litinin bayan lauya mai kare Sowore, Adeyinka Olumide Fusika (SAN) ya ankarar da Mai Shari’a Muhammad Umar kan wasu rahotanni masu cewa SSS na shirin neman a ɗage sauraron shari’ar na dogon zango domin bai wa Sowore cikakkiyar damar shiga babban zaɓen na 2027.

A ranar 30 ga Agusta ne dai SSS ta sanar da cewa Darakta-Janar ɗinta, Oluwatosin Ajayi ya umarci Mista Kehinde da ya ɗauki matakan da suka dace wajen dakatar da shari’ar na wucin-gadi. Ya ce, sun ɗauki matakin ne don bai wa Sowore, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC damar shiga sahun masu yaƙin neman zaɓen 2027. SSS ta kuma ce za a cigaba da shari’ar da zarar an kammala zaɓen, wanda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shirya gudanarwa a Junairun shekera mai zuwa.

Saidai a yayin da aka shiga tattauna batun a ranar Litinin, lauyan SSS ya musanta sanin wannan matsaya, yana mai kira ga kotun da cewa kada ta dogara da rahotannin Soshiyal Mediya da ba a tantance su ba.

By Babaji

Leave a Reply