Shugaban NSIRS ya jaddada ƙudirin kawo sauyin haraji a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Shugaban hukumar haraji ta Jihar Nasarawa (NSIRS), Alhaji Ibrahim Adamu Sarki, ya jaddada aniyarsa ta kawo sauye-sauye a fannin haraji a hukumar.

Sarki ya bayyana kuɗaɗen shiga a matsayin ginshiƙin gina al’umma, inda ya yi alƙawarin cigaba da bin ƙa’idojin kuɗi wajen tara kuɗaɗen shiga domin samun tattalin arziki mai ɗorewa da jihar.

Alhaji Ibrahim Adamu Sarki ya bayyana hakan ne a lokacin wata hira da yayi da wakilin Manhaja a ofishinsa a ranar Litinin na mako da ake ciki inda ya ƙara da cewa ƙudurin hukumar na tara sama da Naira biliyan huɗu a cikin kwanaki 100 na farko na zamansa shaida ce ta jajircewa, aiki tukuru da rikon amana na kuɗi.

Ya jaddada cewa hukumar na aiki tuƙuru wajen cimma hasashen kuɗaɗen shiga na Naira biliyan 50.

Shugaban na NSIRS ya kuma yi amfani da damar inda yayi kira na musamman ga masu biyan haraji a jihar dasu riƙa bin ƙa’idojin biyan haraji domin inganci da ingantaccen aiki yana mai cewa hukumar za ta cigaba da wayar da kawunan jama’a kan muhimmancin biyan harajin da sauran su.

Har ila yau ya kuma yi alƙawarin haɗa kai da manema labarai, hukumomin tsaro, ƙungiyoyi masu zaman kansu da ma’aikatu, sassa da hukumomi (MDAs) a faɗin jihar domin inganta bin haraji, tara haraji da tilasta biya.

Da yake jaddada muhimmancin sauye-sauyen cibiyoyi ga gudanar da haraji, Sarki ya bayyana alaƙar da ke tsakanin ƙwarin gwiwar masu biyan haraji da bin ƙa’idojin kuɗi domin bunƙasar tattalin arziki wajen cimma burin shugabanci.

By ukarofi

Leave a Reply