
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar adawa ta NDC ta zargi Hukumar Zaɓe ta Ƙasa da yin watsi da buƙatarta ta samun damar shiga shafin yanar gizo hukumar da za ta wallafa sunayen ‘yan takararta.
Haka kuma, jam’iyyar na shirin shigar da ƙarar ƙalubalantar hukuncin kotu na soek rajistarta.
Wannan ci-gaba na zuwa ne a daidai lokacin da wata Babbar Kotun Tarayya ta umarci INEC ta soke rajistar NDC, hukuncin da ya jefa jam’iyyar cikin halin rashin tabbas akan sahihancin shigarta zaɓukan da ke tafe.
Sakataren yaɗa labaran NDC, Osa Director ya ce NDC ta buƙaci INEC da ta bata lambobin damar shiga shafinta domin miƙa jaddawalin sunayen ‘yan takararta a yanar gizo, amma hakan bai samu ba.
A cewarsa, jami’an hukumar sun shaida wa jam’iyyar cewa za su dawo gare su, inda suka bar ta cikin zullumi gabanin umarnin sokewar ta kotun.
