‘Yan sanda sun kama wani mutum bisa laifin cin mutuncin Alqur’ani a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama wani mutum mai suna Abubakar Musa ɗan asalin ƙauyen Rafin Mose da ke ƙaramar hukumar Zuru bisa ga laifin cin mutuncin Alqur’ani mai tsarki.

Da ya ke zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja, Kakakin rundunar ‘yan sanda Sufurtanda Bashir Usman ya bayyana cewa an kama wannan mutum ne bisa zargin haɗa baki da Rabi’u Tela da matar sa Zara’u Hassan da kuma Hamza Zango bisa ga laifin surkulle da keta haddin al’umma da kuma cin mutuncin Alqur’ani mai tsarki.

Ya ƙara da cewa bincike ya nuna sauran abokan aikin sa sun sun gudu amma dai an sami waɗansu kaya da suka haɗa da Kafin Alqur’ani da Maniyyi, ja da farin goro, ƙaramar rigar ciki da mushen dabba da sauran kayayyaki da zummar za a haƙa rami a binne su a cikin ɗakin Zara’u Hassan.

Ya ce an yi ƙudirin yi wannan aikin ne bisa ga zummar a mallake zuciyar Zara’u Hassan domin ta zama mai cikakkiyar biyayya.
Kakakin rundunar ‘yan sanda Sufurtanda Bashir Usman ya ƙara da cewa yanzu haka dai ana cigaba da bincike kuma rundunar yan sanda ta baza komar ta don farauto waɗanda suka gudu domin su fuskanci shari’a.

Ya kuma nemi al’umma da su cigaba da bai wa jami’an ‘yan sanda haɗin kai na kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

By ukarofi

Leave a Reply