Yanzu-yanzu: Kotu ta tasa ƙeyar Adeyemin hukumar bogi zuwa kurkuku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci a tura Darakta-Janar na Hukumar da aka ayyana a matsayin “ta bogi”, wato Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), Frins Adeniyi Matthew mai shekaru 38 zuwa kurkukun Kuje da ke birnin tarayyar.

Mai Shari’a Mohammed Umar yayin hukuncinsa a ranar Laraba, ya umarci a ajiye Adeniyi a gidan yarin har zuwa lokacin da za a gabatar musu da buƙatar bayar da belinsa.

Umarnin alƙalin ya biyo bayan da Adeniyi ya musanta baki ɗaya tuhume-tuhume guda takwas da ake masa na makirci da amfani da bayanan bogi da aka gabatar wa kotun akansa da wasu mutum biyu – Femi, wanda ba a san cikakken sunansa ba da Anu, wanda shi ma ba a san ainihin sunansa ba kuma ana cigaba da neman su ruwa-a-jallo.

Sauran bayanai za su biyo baya…

By Babaji

Leave a Reply