Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta karɓi rahoton ƙudirin dokar ƙirƙirar hukumar kula da ilimin sakandire ta Jihar Katsina (Katsina State Secondary School Education Board).
A wani rahoto da aka gabatar na zaman majalisar ƙarƙashin jagoranci kakakin majalisar dokokin Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura.
Shugaban kwamitin Ilimi na majalisar, kuma ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Mai’adua, Hon. Mustapha Rabe Musa, ya gabatar da rahoton tare da yin bayani kan muhimman abubuwan da ƙudirin dokar ya ƙunsa.
Sabuwar hukumar da ake shirin kafawa za ta kasance da alhakin kula da harkokin gudanarwa da bunƙasa makarantun sakandire a faɗin Jihar Katsina, tare da tabbatar da cewa makarantu sun samu abubuwan da ake buƙata domin gudanar da ingantaccen karatu.
Ƙudirin dokar ya kuma mayar da hankali ne wajen samar da ingantaccen tsarin kula da ilimin sakandire, da kuma inganta yanayin koyarwa da koyo a makarantun jihar.
Idan aka tabbatar da dokar hukumar za ta taka muhimmiyar rawa wajen daidaita da kuma kula da harkokin makarantun sakandire a faɗin jihar, musamman wajen samar da kayan koyarwa, kayan aiki da sauran abubuwan da ake buƙata domin inganta ilimin ɗalibai.
Manufar ƙudirin dokar shi ne ƙara inganta ilimin sakandire a Jihar Katsina, ta yadda ɗalibai za su samu ingantaccen yanayin karatu, malamai su samu abubuwan da suke buƙata wajen koyarwa, sannan makarantu su samu kulawar da ta dace.
Ƙudirin dokar dai na ci gaba da bin matakan da suka dace a majalisar dokokin Jihar Katsina kafin kammala tsarin ƙirƙirar hukumar.
