Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
’Yan bindiga sun kashe mutane takwas a yankin Maigora da Sabon Layi a ƙaramar hukumar Faskari a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne sakamakon wani saɓani da ya biyo bayan kama wani mai mashin, wanda ya ɗauko wasu mutane da kuɗi wanda ake zargin kudin fansa ne, akan hanyar Maigora lamarin da ya sa aka kama mutanen tare da tsare su.
Kamar yadda kafar sadarwa na BBC ta ruwaito lamari ya harzuka ’yan bindigar yankin, inda suka kai hari kan mutanan da basu jiba basu gani ba suka halaka mutum takwas, sannan suka yi garkuwa da wasu mutane 38.
Sai dai rahotanni na baya-bayan nan sun bayyana cewa an saki mutanen 38 da aka yi garkuwa da su, sakamakon shiga tsakanin masu sasanci a yankin.
