Ɗan Ministan Abuja ya miƙa fasfonsa ga kotu kan zargin damfarar filin Dala 2.1m

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba Jordan Wike, wanda ɗan Ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya gabatar wa Babbar Kotun Abuja fasfo ɗinsa na Amurka yayin da yake cigaba da kariyarsa a shari’ar da ta ƙunshi zargin damfarar Dala miliyan 2.1 na samar da wani fili a Abuja.

Manhaja ta ruwaito cewa, a ranar Litinin ne Alƙali Sylvanus Oriji na kotun ya umarci Jordan da ya gabatar da fasfo ɗinsa na Amurka bayan wani rikici kan inda yake a ranar 25 ga Oktoba, 2025, ranar da masu iƙirarin suka yi zargin ɗan ministan ya karɓi miliyan $2.1 a tsabar kuɗi daga gare su a wani gida da ke Gwarimpa a Abuja.

Wani Safwan Garba GY da GY Global Oil & Gas Nigeria Limited ne suka shigar da ƙarar, inda ya suka yi zargin cewa Jordan ya karɓi tsabar kuɗin daga gare su a shekarar da ta gabata domin shige musu gaba wajen mallakar manyan filaye guda biyu a wasu fitattun unguwannin Abuja, zargin da ɗan ministan ya musanta.

A cewar jaridar Premium Times, Jordan ya ce ya bar Nijeriya da fasfonsa na Amurka a ranar da masu iƙirarin suka ce sun ba shi kuɗin. Sai dai a nasu ɓangaren, sun ce ya fara fafutukar samar musu fili ne bayan sun haɗu da shi a Landon sun ƙulla alaƙa. Sun yi zargin cewa, Jordan ya amince da samar musu da fili mai faɗin hekta 30 a Katampe da Guzape akan jimillar kuɗi Dala miliyan 2.1. An zargin ɗan ministan da shaida wa masu ƙarar cewa miliyan $2 na mahaifinsa ne yayin da $100,000 kuma nasa ne.

Sannan, ɓangarorin sun ce sun ba shi tsabar kuɗin ne a ranar 26 ga Satumbar 2025 akan idon wani Adamu Sani, Aliyu Sarki da kuma Sai Wani. Haka kuma, wani Onor Sandy yana gurin da abin ya faru hasali ma shi ne ya yi wa Jordan rakiyar zuwa wajen.

Waɗannan ɓangarori dai sun yi iƙirarin cewa Jordan da mahaifin nasa wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, ba a iya samun damar ganawa da su gaba da gaba ko ta wayar tarho bayan karɓar kuɗin. Kuma sun gano cewa filayen da aka musu alƙawarin samu, na wani kamfani ne da ke ƙoƙarin fara aiki akansu. Kazalika, sun ce sun nemi a dawo musu da kuɗin nasu a ranar 31 ga Oktoba, 2025 amma ba su samu gamsashshiyar amsa ba, lamarin da ya tilasta musu shigar da ƙara domin a dawo musu da kuɗinsu.

A yayin zaman na Laraba, Jordan ya gabatar da fasfon nasa na Amurka ga kotu ta hannun lauyansa, Ogwu Onoja (SAN) domin a yi nazari a kai yayin da yake ƙoƙarin wanke kansa ta yadda akwai yiwuwar ya yi nasara muddin jaddawalin zirga-zirgarsa ya saɓa da ranar da waɗancan suka yi iƙirarin damƙa masa kuɗin.

By Babaji

Leave a Reply