Cardoso, Ojulari da Tantita za su halarci taron Karramawa na Blueprint gobe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso; Shugaban Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Injiniya Bashir Bayo Ojulari da Kamfanin Tantita Security Services suna daga cikin sanannun mutane da ƙungiyoyin da za a karrama a babban taron shekara-shekara na bayar da lambobin yabo da Kamfanin Jaridun Blueprint Newspapers Limited zai jagoranta a gobe Talata, 18 ga Agusta, 2026.

Taron, wanda za a gudanar a ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre, Abuja, zai haɗa manyan jami’an gwamnati, jagororin siyasa, jagororin kamfanoni, masana harkar tsaro, ‘yan difulomasiyya, malamai, wakilan ƙungiyoyin al’umma, da wasu masu ruwa da tsaki.

Cardoso zai karɓi kyautar ‘Financial Sustainability and Regulatory Oversight Award’, wato na ƙoƙarinsa a fannin ɗorewar kuɗi da sanya ido kan gudanarwa a babban bankin da kuma ƙoƙarinsa wajen ƙarfafa ɗorewar kuɗaɗe da sanya ido kan lamuran gudanar da su a tsarin harkar banki a Nijeriya.

Shi ma Ojulari na NNPCL, zai karɓi kyautar ‘Corporate Leadership Award’, bisa ƙoƙarinsa a harkar gudanar da babban kamfanin man na ƙasa da gudumawarsa na ƙoƙarin dawo da martabar harkar Kamfanin makamashi wajen inganta harkokinsa da tabbatar da gaskiya da adalci acikin haka.

Shi kuwa kamfanin Tantita, zai karɓi kyautar ‘Outstanding Security Surveillance’ bisa gudumawarsa kan harkar sanya ido da bayar da kariya ga fannin mai da gas a Nijeriya.

Ayyukan kamfanin a yankin Neja-Delta sun taimaka wa ƙoƙarin gwamnati na kakkaɓe ayyukan satar ɗanyen mai, lalata bututun mai da wasu haramtattun ayyuka da ke haifar da koma-baya ga harkar samar da fetur, kuɗaɗen shiga da tsaron muhalli.

Waɗannan kyaututtuka da Blueprint Newspapers Limited ya shirya bayarwa, wani ɓangare ne na ƙoƙarin yaba wa ƙoƙarin mutane da cibiyoyin gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu waɗanda ayyukansu suka samar da kyawawan sakamako a fannonin shugabanci, kuɗi, gudanarwar haɗaka, tsaro da kuma ci-gaban ƙasa.

By Babaji

Leave a Reply