Adeleke ya janye ƙarar EFCC bayan nasara a zaɓen Osun

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wanda aka sake zaɓa a matsayin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya ce ya umarci Antoni Janar na jihar da ya janye ƙarar da suka shigar akan Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, bisa rufe asusun bankin gwamnatin jihar gabanin zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.

Adeleke ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, sa’o’i bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da Hukumar Zaɓe (INEC) ta yi.

Yayin da aka masa tambaya kan halin batun rikicin siyasa da na EFCC bayan sake lashe zaɓen, gwamnan ya ce ya yanke shawarar cigaba da gudanar da harkokinsa bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsoma baki akan lamarin.

A baya dai gwamnan ya ƙalubalanci matakin EFCC na umarnin a rufe asusun gwamnatin jihar, yana mai bayyana hakan a matsayin abin da aka siyasantar da da kuma ƙoƙarin hargitsa harkokin gwamnatin nasa.

Daga bisani a washe-garin ranar Shugaba Tinubu ya umarci hukumar yaƙi da rashawan da ta cire takunkumin da ta sanya wa asusun da kuma daina ɗaukar dukkan wani matakin shari’a a kai, bayan ya koka kan lokacin da aka ƙaddamar da matakin, wanda ya zo kusa da zaɓen gwamnan jihar.

Game da zargin cewa EFCC ta gayyaci wasu magoya baya da jami’an gwamnatinsa kan amsa wasu tambayoyi, Adeleke ya ce ya umarci lauyoyinsa da su bayar ba’asin dukkan abin ya dace kan al’amarin. Ya kuma ce hukumar ta gayyaci wasu mataimakansa, waɗanda daga bisani ta sako su kasancewar ba a same su da laifin komai ba.

A farkon watan Agusta ne EFCC ta rufe asusun gwamnatin na Osun a matsayin wani ɓangare na bincike kan zargin damƙa wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai kusan Naira biliyan 11 a kuɗaɗen kula da muhalli, kuɗaɗe tallafin ayyukan ababen more rayuwa da na Asusun Kuɗaɗen Tarayya (FAAC).

EFCC dai ta ce ta ɗauki matakin ne bayan gano hada-hadar wasu kuɗaɗe masu alamar tambaya, lamarin da ya sa ta dakatar da ƙarin wasu hada-hada yayin da take bincike.

By Babaji

Leave a Reply