
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa saƙonsa na taya murna ga ɗaya daga cikin manyan ƙasa kuma tsohon shugaban mulkin soji na Nijeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) yayin da ya cika shekara 85 duniya a ranar 17 ga Agusta, 2026.
Tinubu ya bayyana IBB a matsayin jajirtaccen jagora wanda horonsa na aikin soja ya yi gagarumin tasiri a harkar shugabancin Nijeriya bayan juyin mulkin 1985. Shugaban ya bayyana haka ne a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun kakakinsa Bayo Onanuga, ranar Lahadi.
A cewarsa, tsohon shugaban ƙasar ya yi wa Nijeriya tasirin da wani shugaba bai taɓa yi ba a tarihi, yana mai cewa shekarunsa takwas sun ƙarfafa lamuran siyasa, tattali da ci-gaban taswirar ƙasa.
Ya ce, Babangida ya faɗaɗa fannin tattali, samar da ababen more rayuwa masu ɗorewa da kafa hukumomi da cibiyoyi da dama don cigaba da hidimta wa Nijeriya. Hikima da hangen nesansa da ƙoƙarin samar da daidaito ya sa aka samu wasu jihohi a faɗin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya kuma ce sunan da IBB ya yi da kyawawan ayyukan da ya shumfiɗa za su cigaba da zama ginshiƙi a tarihin ci-gaban Nijeriya saboda gudunmawarsa masu tarin yawa na ci-gaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa, hatta a shekarunsa na ritaya yayin da yake zama a gidansa na Minna, Jihar Neja, Babangida na cigaba da nusarwa da bayar da shawara kan muhimman al’amuran ƙasa.
A ƙarshe, ya yi masa fatan cigaba da kasancewa cikin ƙoshin lafiya da fatan Allah Ya ƙara masa shekaru masu albarka.
