
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shahararren mawaƙin Nijeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido, ya goge wasu wallafe-wallafen siyasa guda biyu a ranar Asabar 15 ga Agusta, 2026, lamarin da ya jefa masoya da masu sharhi kan harkar siyasa ƙalubalantar dalilinsa na ɗaukar matakin.
A ɗaya daga cikin rubutun nasa, Davido ya bayyana cewa daga yanzu iyalansa ba za su sake goyon bayan wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba, inda ya sanya hoton kawun nasa kuma gwamnan Jihar Osun a gefen rubutun.
A wata ɗaukar fuskar salula ta nuna cewa Davido ya goge wani rubutun ya yi ishara da Shugaba Bola Tinubu, inda ya rubuta “U no try @officialABAT.”
Duk da cewa an goge wallafa biyun jim-kaɗan bayan ɗora su, an yi ta yaɗa ɗaukar rubutun a kafafen sada zumunta, lamarin da ya ba dubunnan masu amfani da Soshiyal Mediya damar buɗewa da kuma yaɗa su.
Kasancewar Davido na da alaƙar dangi da siyasar Jihar Osun, hakan ya sa kalamansa a kafafen sadarwa suna tasiri a fannin. Haka kuma, alaƙar siyasar Gwamna Adeleke da Shugaba Tinubu ta zama abin tattaunawa cikin al’umma, wanda hakan ya sa dukkan wani ra’ayi na rashin jituwa acikin iyalan ya zama mai matuƙar muhimmanci gabanin zaɓuka na nan gaba.
Ga kaɗan daga cikin tsokacin da wasu suka yi kan matakin goge rubutun na mawaƙin kamar yadda jaridar IntelRegion ta wallafa:
“@Lingardobi said; “He’s fighting for his family, Osun State Government House is their family business.”
@lade_badboii shared; “That statement alone fit implicate him uncle now. Cuz this election self, the very likely outcome will be inconclusive. Abii no be the same Osun wey I sabi? No be everything be cho cho cho. At least he’s old enough. Hin suppose get filter for mouth now.”
@ojumah uttered; “You know how many calls him papa go don call am for that tweet.. David’s tweet’s all day has proven just one thing, everybody is tired of the APC… He has used his influence for good today alongside the Osun people.. let’s all use ours come the presidential elections..”
@Titu6286 noted; “Their foolish supporters will attack you for calling them out. He’s part of the problem we are having in Nigeria.”
@Rinsole_T stressed; “He wasn’t supposed to put that out.. Even if he’s not supporting anyone..it’s supposed to be secret till the present election is over.”
