
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Edo, Blessing Agbebaku ya sauka daga muƙaminsa yayin da ake tsaka da zargin wasu mambobin majalisar na shirin tsige shi.
Rahotanni sun bayyana cewa, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Akoko Edo ta II, Yekini Idaiyi ne aka rantsar a matsayin sabon kakakin bayan matakin na Agebakun.
Mai taimaka wa Agbebaku kan harkokin yaɗa labarai, Ivy Ebojele ne ya tabbatar da murabus ɗin mai gidan nasa a wani rubutu da ya ɗora a kafar Facebook a ranar Litinin, inda ya ce za a fitar da ƙarin bayani kan al’amarin a lokacin da ya dace.
A watan Yunin 2023 ne aka naɗa Hon. Agbebaku, wanda ke wakiltar mazaɓar Owan ta Yamma a matsayin kakakin.
An fara rikici da shi ne a watan Mayun 2024, jim-kaɗan bayan ya dakatar da ‘ya’yan majalisar guda uku kan zargin su da yunƙurin tsige shi tare da wasu manyan mambobin Majalisar. A lokacin ne ya yi iƙirarin cewa an kai layu da wasu ababen tsafi cikin farfajiyar majalisar yayin zargin kitsa makircin tsige shi a kujerar.
Haka kuma, waɗanda ya dakatar na hannun dama ne ga tsohon mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu da wani na hannun daman Adams Oshiomhole (tsohon gwamnan jihar), wanda shi ne ake ɗauka a matsayin Uban gidan Gwamna mai ci a yanzu na jihar, wato Monday Okpebholo. Saidai, ‘yan majalisar da aka dakatar sun musanta zarge-zargen, inda suka bayyana matakin da wata manufa ta siyasa.
A watan Mayu, 2025 ne Agbebaku ya koma jam’iyyar APC daga PDP bayan wasu jiga-jigan APC sun nemi a cire daga muƙamin kakakin, inda suka nemi a ɗauki ɗan APC daga yankinsa don ya maye gurbinsa.
