JIBWIBS a Katsina ta bada umarnin gabatar da alqunut

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Ƙungiyar jama’atu izalatil bidi’a ea ikamatis sunnah ta Jihar Katsina ta bada umarnin gabatar da al-qunut a faɗin jihar Katsina.

Wannan mataki da ƙungiyar ta ɗauka ya biyo bayan taron da ya gudana na majalisar zartaswa ta ƙungiyar domin nazarin halin da ake ciki a jihar Katsina tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen samar da mafita mai ɗorewa ga ƙalubalen da al’umma ke fuskanta.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban ƙungiyar Sheikh Yakubu Musa Hassan (Sautus Sunnah) ya bayyana cewa manufar kiran wannan taron ita ce tattauna manyan matsalolin da suka addabi al’umma, musamman matsalar rashin tsaro da taɓarɓarewar tarbiyya, tare da tsara hanyoyin da za su taimaka wajen samun mafita bisa koyarwar Al-Qur’ani da Sunnah.

Shugaban ya kuma yi ishara da taron da Gwamnatin Jihar Katsina ta kira shugabannin ƙungiyoyin addini da malamai domin neman shawarwari kan hanyoyin magance matsalar rashin tsaro da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Bayan dogon nazari, majalisar ta bayyana cewa Allah (S.W.T) ya hore wa al’umma matasa masu ƙwazo waɗanda za su iya taka muhimmiyar rawa wajen shiryar da jama’a, dawo da kyawawan ɗabi’u, yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, da kuma magance matsalar baɗala.

Majalisar ta kuma jaddada cewa gyaran al’umma ba zai cika ba sai an samar da shugabanci nagari. Saboda haka, ta ƙarfafa mambobinta da sauran al’umma su shiga cikin harkokin siyasa domin samar da shugabanni na gari tun daga matakin farko, domin a samu jagoranci nagari a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Ya ce kungiyar ta amince da aiwatar da wani shiri na dogon zango da zai mayar da hankali kan wayar da kan al’umma, gina tarbiyya, da ƙarfafa shugabanci nagari.

Shirin a cewar sa zai mayar da hankali kan gina ilimi a matsayin jigon addini da zaman lafiya.

Sai fahimtar al’amuran zamani bisa koyarwar Musulunci (Fiqhul Waqi’) da haɗa ƙarfi da ƙarfe domin magance matsalolin da su ke fuskantar wannan al-umma.

Wasu ƙudirin da ƙungiyar ta cimma kamar yadda Sheikh Yakubu Musa ya sanar shine, gina tarbiyya da ƙarfafa imani ga matasa da wayar da kai kan haƙƙoƙin maƙwabtaka da zamantakewa a tsakanin al’umma.

A wajen taron an gabatar da ƙasidu kan muhimmancin kishin ƙasa da rawar da ake takawa wajen gina al’umma da gudummawar mutanen kirki a harkokin siyasa da wajabcin shiga domin gyaran al’umma saboda matsalolin taɓarɓarewar tarbiyyar matasa da hanyoyin magance su da sauran su.

A ƙarshe, majalisar zartaswa ta ƙungiyar a Jihar Katsina ta amince da bada umarnin gabatar da al-qunut a dukkan masallatan ƙungiyar da ke faɗin jihar Katsina.

An umarci cewa za a riƙa gabatar da al-qunut a dukkan sallolin farilla guda biyar, tare da yin addu’o’i na musamman kan halin rashin tsaro da sauran ƙalubalen da al’umma ke fuskanta. Haka kuma, za a ci gaba da yin irin waɗannan addu’o’i a ƙarshen huɗubobin Juma’a kamar yadda aka saba.

Taron ya gudana ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na Jihar Katsina, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah), tare da halartar dukkan masu riƙe da muƙaman ƙungiyar a matakin ƙasa da na jiha, shugabannin ƙananan hukumomi da sakatarorinsu, shugabannin majalisar malamai na ƙananan hukumomi da sakatarorinsu, shugabannin majalisar agaji na ƙananan hukumomi da sakatarorinsu, da kuma shugabannin kwamitin limamai na ƙananan hukumomi.

By ukarofi

Leave a Reply