Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin wutar lantarki ga ’yan Nijeriya.
A zaman majalisar na ranar Labara ne ta amince wa Shugaba Bola Tinubu ya karɓo bashin daga Bankin Duniya.
Bayan karɓar rahoton kwamitin basukan kasashen waje ne majalisar ta amince da karɓo bashin wanda za a damƙa ga Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE).
Bashin Dala miliyan 500 da za a sayi mitocin lantarkin da su wani ɓangare ne na bashin Bankin Duniya na Dala biliyan 7.94 da Tinubu ya samu anincewar majalisar da zai karɓo a ƙarƙashin tsarin karvar basukan ƙasashen waje na 2022-2024.
Da yake gabatar da rahoton, mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Haruna Manu, ya ce kuɗaɗen da mitocin za su taimaka wajen ingata samun wutar lantarki a ƙasar.
A cewarsa, aikin samar da mitocin zai ƙara ingantar ƙarfin kamfanonin rarraba wutar lantarki da kuma samun kuɗaɗen shiga a gare su.
