Za mu gurgunta samar da fetur muddin ba a biya mu bashin N200bn ba — IPMAN

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Masu Dakon Fetur ta Nijeriya (IPMAN), ta yi barazanar gurgunta samar da fetur afaɗin ƙasa muddin ba a biya ta bashin Naira biliyan 200 da take bi ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙarancin fetur ke ci gaba da ta’azzara lamarin da ya yi sanadiyar ƙarin farashin fetur a sassan ƙasa, inda a yanzu ake sayar da fetur tsakanin N610 da N800 kan lita guda a wasu wurare, sannan N1000 zuwa N1200 a kasuwar bayan fage.

Jigo a IPMAN, Mazi Oliver Okolo ne ya yi wannan barazanar, kuma cewa da goyon bayan shugabancin IPMAN na ƙasa ya faɗi hakan.

Okolo ya ce bashin da suke bi ɗin ya rataya ne a kan hukumar kula da fetur, wato Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Commission (NMDPRA).

A cikin bayanin bayan taron manema labarai da ya fitar a ranar Talata, Okolo ya ce hukumar NMDPRA ta gagara biyan su bashin da suke bi duk da umarnin da Ministan Fetur, Heineken Lokpobiri, ya bayar kan a biya kuɗaɗen.

Ya ƙara da cewa, tun bayan da Ministan ya ba da umarni a watan Fabrairun da ya gabata, Naira biliyan 13 aka biya mambobinsu.

Ya ce rashin biyan kuɗaɗe ya haifar wa mambobinsu cikas matuƙa wajen gudanar da harkokinsu.