Ta ya za ku iya ƙara wa ƙwaƙwalwarku kaifi?

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa tare. A wannan makon shafin kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja zai yi duba ne kan muhimmin abu da lafiyar jikinmu ke buƙata ko in ce jiki ke buƙata don tabbatar da gudanar da ayyukan yau da kullum ba tare da matsala ba. Ba komai nake magana kai ba face kaifin ƙwaƙwalwa.

Ƙwaƙwalwar ɗan adam wata halitta ce mai cike da abin ban mamaki, kuma muhimmancinta ga jikin mutum lamari ne mai gima. Duba da cewa kusan kowacce gava ta jikin ɗan adam tana da hedikwata a ƙwaƙwalwa, wadda daga can ne take kitsa komai kafin ya kasance.

Wannan ne ya sa ƙwaƙwalwa ke ɗauke da biliyoyin jijiyoyi, waɗanda suke isar da saƙonni zuwa kowanne ɓangare na gangar jiki.

Idan mun dubi yanayin yadda zamani ke canzawa da yadda ababen yi ke ƙara yawaita ga mutane da kuma ƙarancin lokaci da muke da shi, za mu fahimci wannan darasi na da matuƙar muhimmanci kasancewar ayyukan da muke buƙatar aiwatarwa dole za su zama cikin hanzari kasantuwar lokaci da ke gudu, wanda hakan na nufin buƙatar hanzartawa daga ƙwaƙwalwa.

Bari mu fara da matsalar damuwa, wadda zuwa yanzu da yawa mun samu masaniya kanta da yadda take tasiri a rayuwarmu bakiɗaya, ciki kuwa har da raunana kaifin ƙwaƙwalwa.

Don haka ga mai wasu alamomin cutar damuwa, za mu ce magance ta ce hanya babba da zata kai ka ga haɓaka kaifin ƙwaƙwalwa.

Yana daga cikin hanyoyin da za a iya ƙarfafa qwaqwalwa samun hanyoyin faranta rai, ma’ana a cikin duk abinda ka ke yi na rayuwa, duk yadda rayuwarka take a cike da ayyuka, ka tabbatar ka samu aikata wani abu da ranka ke so a kowacce rana, ya Allah kallo ne, karatu ne, ƙwallo ko makamantansu.

Ya kasance ba ka mayar da ƙwaƙwalwar injimin aiki a kodayaushe ba. Samun farin cikinka tamkar watsa ruwan sanyi ne ga injimin da ya yi zafi sakamakon jimawa yana aiki.

Wannan kuwa ba iya kaifin ƙwaƙwalwa alfanun sa ya tsaya ba, domin kariya ce daga kamuwa da cutar mantuwa, ko dakushewar ƙwaƙwalwa ko ince rashin fahimta ko gane karatu.