Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyoyin gasar Firimiyar Ingila za su kaɗa ƙuri’ar amincewa ko akasin haka kan cigaba da amfani da na’urar VAR mai taimaka wa alƙalin wasa a wata mai zuwa.
Kulob ɗin Wolves ya miƙa ƙudiri a hukumance zuwa ga hukumar firimiya, abin da zai sa a kaɗa ƙuri’ar lokacin da mambobin gasar za su gana ranar 6 ga watan Yuni.
Ƙungiyar ta ce an ƙaddamar da VAR ɗin ne da “kyakkyawar manufa” amma kuma ta koma jawo abubuwan da ba a nufata ba da ke lalata alaƙar ‘yan kallo da wasan ƙwallon ƙafar”.
An fara amfani da VAR a 2019 domin taimaka wa tawagar alƙalan wasa da ke cikin fili yanke hukunci, amma kuma an samu matsaloli da wasu hukunce-hukuncen a wannan kakar.
“Matsalar da muke samu wajen ba da hukunci daidai bai dace da al’adar wasanni ba,” inji sanarwar da Wolves ta fitar.
