Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kimanin malamai da limaman Juma’ah daga ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina suka jaddada goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Malaman sun bayyana goyon bayansu a wani gagarumin taro da ya gudana tare da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa Siyasa Alhaji Kabir Ibrahim Masari da ya wakana a ɗakin taron na Paragon Event Center a Katsina
A jawabin sa, Alhaji Kabir Ibrahim Masari ya ce a dukkanin ƴan takarar shugaban ƙasa babu wanda ya cancanta a sake zaɓe a karo na biyu kamar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Alhaji Kabir Ibrahim Masari ya nanata cewa da iznin Allah ranar 18 ga watan Janairun 2027, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai zarce karo na biyu a neman wa’adi na biyu na mulkin Nijeriya.
A nashi jawabin, ministan gidaje Injiniya Muttaka Rabe Darma ya yi kira ga malaman da su shirya wa’azozi da hudubobi tare da gaya wa mutane abinda yake gaskiya kuma wanda ya kamata a zaɓa.
Ministan yace kasancewarsu malamai dake da daraja a fuskar jama’a babu waɗanda suka cancanta su shiga gaba a sanarwa mutane zaɓen musulmi da musulmi kamar su.
A jawabinsa, Shugaban hukumar AUDA-NEPAD Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri ya yi kira ga malaman da su ƙara faɗakar da jama’a akan cancantar zaɓen Bola Ahmed Tinubu.
A jawabin su daban-daban, Farfesa Abdul’aziz Ahmed Mashi da Sheikh Hadi Balarabe da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan da Sheikh Abu Ammar, sun karanto ayoyin Alkur’ani tare da nusar da mutane akan cancantar zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Shima a nashi jawabin,ɗan majalisar wakilai Hon. Sani Aliyu Ɗanlami yace duk ayyukan da ake shimfida wa Tinubu ne ya turo su, sannan dukkanin ƴan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Peter Obi babu wanda ya taɓa jajanta wa mutane Rt Hon. Aliyu Sabiu Muduru da Injiniya Shehu Garba Matazu da sauransu.
Malamai da limamai da suka halarci taron sun fito daga kungiyoyin ɗarikar da izala a Jihar Katsina.
