Gwamna Raɗɗa ya tabbatar da yin cikakken bincike kan kisan Masussuka

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya yi jimamin kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, inda ya bayyana shi a matsayin murya mai kira ga zaman lafiya, zaman tare da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

A wata sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai na Gwamnan mohammed Kaula ya fitar gwamnan ya tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike kan yadda aka kashe shi.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe malamin ne tare da wani abokinsa da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba, waɗanda ke kan babura, a wajen gidansa da ke ƙaramar hukumar Dutsin-Ma a daren ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana matuƙar kaɗuwarsa kan wannan lamari, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, al’ummar Musulmi da dukkan waɗanda wannan rashi ya shafa.

“Ina kira ga iyalan mamacin da su yi haƙuri, su miƙa al’amarinsu ga hukuncin Allah maɗaukakin sarki, tare da ƙarfafa imaninsu a wannan lokaci mai wahala. Ina roƙon Allah ya ba su ƙarfin zuciya da haƙurin jure wannan babban rashi,” in ji shi.

Gwamnan ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su ƙara ƙaimi wajen gudanar da bincike kan kisan, gano waɗanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su a gaban shari’a domin su fuskanci hukuncin da ya dace.

“Dole ne a hukunta waɗanda ke da hannu a wannan mummunan aika-aika. Ina kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan laifi sun fuskanci cikakken hukuncin doka,” in ji gwamnan.

Ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su kwantar da hankalinsu, su ba hukumomin tsaro haɗin kai tare da bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gudanar da bincike. Ya kuma gargaɗi jama’a da su guji duk wani mataki da zai iya ƙara tayar da hankali ko kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana Sheikh Masussuka a matsayin malamin addinin Musulunci da aka san shi da koyarwa bisa Alƙur’ani, yaɗa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban, da kuma adawa da tsattsauran ra’ayi, ta’addanci da tsattsauran koyarwar da ke iya jawo rikici.

Gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta wa mamacin, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, tare da ba iyalansa, abokan hulɗarsa da daukacin al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi.

By ukarofi

Leave a Reply