Malamai sun yi wa ƙabilanci guduma a Kano

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Idan ka ji manya irin Farfesa Aliyu Muhamma Bunza na cewa in Rabaran Shu’aibu Bargi ya nemi kuɗi biliyan 10 zai samu daga masu zagon ƙasa ga Arewa don sai ka daki juji don jin ƙarar gwazarmar dala nawa zallawa ke samu.

Haƙiƙa a taron malamai da asusun INƙAAZ ya shirya a Kano don bayyana illar ƙabilanci, Shehun malamin harshen Hausa Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya yi jawabi mai muhimmanci na hasashen idan Sarkin Hausawa Kirista Rabaran Shu’aibu Bargi ya nemi kuɗi biliyan 10 ba mamaki Naira ne zai samu daga masu shiryawa Arewa zagon ƙasa. Gaskiya na lura a lokacin ba kowa ya san labarin naɗa Rabaran Shu’aibu Bargi sarautar Hausawa mabiya addinin Kirista na Kano ba sai da Farfesa Bunza ya kawo maganar. Wannan kuwa ba mamaki ya faru ne don a wani keɓantaccen ɗakin taro ne da ma’abota BAHAUSHE YA MULKI KANSA su ka yi cincirindo a ka ɗaura rawanin.

Farfesa Bunza ya ce yanzu Kano na da sarakuna 3 da su ka haɗa da mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, mai martaba Khalifa Sunusu Lamido Sunusi sai Rabaran Shu’aibu Bargi. Ba na ganin Sarki Aminu ko Khalifa Sunusi za su nemi biliyan 10 daga masoya Kano su samu haka kurum don hidimar yau da kullum, amma Farfesa Bunza ya yi hasashen Bargi zai iya samu. Hakan na nuna yiwuwar waɗanda ke marawa Bargi baya ba wai su shugaban ƙungiyar “Hausa Christian Development Initiative” HACDI Farfesa Daniel Danladi Musa ba ne kaɗai, akwai wasu hamshaƙai a bayan fage. Kuma yadda ma mutum zai gane sun yi naɗin ba tare da sanarda fadar mai martaba Sarkin Kano ba, ba wanda ya godewa fadar mai martaba Sarki. Yo a Kano kamar sauran masarautun Arewa akwai Sarakunan Ibo, Yarbawa, Igala da sauransu amma shi wannan Sarki Bargi mai zaman kansa ne don ba mamaki zai iya nada hakimai da dagatai da sauran manya irin su Galadima da Sarkin Dawaki mai tuta.

Ashe su Daniel sun so Farfesa Bunza ya halarci taron don sun tura ma sa kuɗin jirgi na zuwa da dawowa ba kamar yadda a taron malamai a ka ce kawai ya taho daga Sakkwato ba. Bunza ya ce ya yi dabara inda ya buƙaci su turo ma sa lambar “account” don ya zuba gudunmawarsa, sai ya mayar mu su kuɗin don ya ce ba zai halarci taron nada Sarkin Kirista alhali bai aske gemunsa ba. Kazalika Bunza ya tabbatarwa su Bargi ba za su yi nasara kan Musulmin Kano ba.

Shin Zallawa daga mika asusu a zuba taro sisi ko sayarda fom ɗin rejista N5000 su ke samun kuɗi ko dai iya cin hatsi ne akwai hanyoyin kuɗin shiga? Kai akwai zargi wallahi don na ga Zallewar Zallawa hatta bayan taron malaman, har wani ma da ya nada kansa malamin zallawa ya fara raddi. Ya kamata hukumomin tsaro su binciki yadda wannan harka ta Zalla ko ZAL-TSAN ke tafiya don gudun kar a yi wa Arewa da kasa FAFALOLO wato sakiyar da ba ruwa. AIFOB na kashe dala 60,000 duk wata a Amurka ga masu bin sawu don gwamnatin TUROM ta amince da kafa Biyafara. Ga shi ta tabbata akwai alaka kai tsaye tsakanin Zallawa da AIFOB- TAMBAYA-shin nawa AIFOB ke kashewa a Arewa don aikin zallanci?

Bayan wannan gagarumin taro na wuni daya na malamai mutum mai nazari zai yi mamaki in akwai sauran mai inkirari kan manufar zallawa, yaƙi da Musulunci ne. In su na ja-in-ja su kawo tarihinsu mu san su ‘yan gidan waye ne kuma da a ka mu su mene ne?

A gurguje na ga Zallawa na tsintar abun da ya mu su daɗi daga taron na Kano kan illar ƙabilanci. Kame-kamen shi ne ba su dau jigon taron da ya tabbatar da abun da su ke yi mugun abu ne kuma ba ma shi da alaka da wata sata, kisa ko wata damuwa ta Hausawa. Malamai sun ɗau gudumar hujja sun doka a tsakar uwar makerar ha’inci an ga Zallawa na lilo tsakanin munafurci da zindiƙanci da kuma babbar magana aikin kwangilar maƙiya Arewa.

Wasu na cewa an ji Shehun malamin Hausa Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na cewa Shehu Mujaddadi bai gina masallaci ba! Wallahi sun juya ma sa magana don abun da ya faɗa shi ne ba wani masallaci daban ko a Sokoto na Shehu don masallaci na Musulmi ne. Wannan ma martani ya yi wa Zallawa da ke cewa akwai masallatai ko limaman Fulani ko Hausawa. Masallaci na mai sallah ne ko da Emma Fawaful ne in ya musulunta.

Shin in a na maganar kafa Daular musulunci dungurungum, ai masallaci da makaranta da dakunan adana littafai duk na ciki. Bayan shekaru 209 da rasuwar Shehu, masallatai nawa almajiransa su ka gina. Na kawo faifan bidiyo na ziyarar Sultan Ilori kuma kun ga duk addu’ar da a ka yi ga Shehu ne da irin aikin alheri na karfafa ruhin musulunci. Shi kansa Farfesa Bunza ya ce ya karu da taron har ma ya janye wasu daga abubuwan da ya so gabatarwa. Shin ba su ji wajen ba ne? munafukai.

“AL INƙAAZ CHARITY FOUNDATION” da ya shirya taron wani asusu ne ko ƙungiya da ta ga ya dace ta gayyaci malamai don tattaunawa kan wannan darasi. Haƙiƙa wannan abun farin ciki ne ainun kuma mu na yi wa asusun fatan alheri da tsammanin cikin yardar Allah za a cigaba da gudanar da irin waɗannan taruka duk da tara malamai daga sassa daban-daban ba abu ne mai sauƙi ba. Mu dai al’ummar Arewa mu na sauraron faɗakarwa daga malamanmu kuma mun ji daɗi da su ka dau wannan darasi kamar yadda wasu a cikinsu ke ta ƙoƙarin wayar da kan al’umma ba gajiyawa duk da zaginsu da maƙiya zaman lafiya ke yi.

Gaskiyar magana yanzu mun ga matsayar malamai da Arewa kan wannan batu inda a gefen tsaro a ke kira da babbar murya a yaƙi ‘yan ta’adda kuma a yaƙi goga ƙabilabci ga ta’addanci don amfani da hakan ga biyawa makiya Musulunci na kafa ƙasar ‘yan aware ta Biyafara da ba da dama Midibelawa/Mishan su haɗe da Emma Fawaful. Shin ABOKI zai canja daraja a idon ‘yan Biyafara ko zai ci gaba da zama Malam, Malo, Almajiri, Islmization da sauransu? Hatta ‘yan mishan din na Arewa da ke neman cusa kansu fadar Mazi na da wannan tabon na su ba jinin anyamuri ba ne don haka waƙe-waƙe ne gayyar soɗi karya ludayi ki biya kwano ‘yan arufta Bora a gidan Mowa.

A nan ya na da kyau su ma mabiya addinin Kirista su kira taro don fadar illa ko rashin illar ƙabilanci a Baibul. Hakan zai sa mu gane shin zallawa/mishan Kiristanci su ke yi ko sun fake da addinin ne don samun ‘yancin ƙabilanci inda hakan shafa bakin fenti ne ga addini mai littafi.

Taron nan na Kano da asusun INƙAAZ ya shirya kan illar ƙabilanci ya sa masoya ƙabilanci sun shiga kame-kame wai a yi taro kan illar “bandits” ga Musulunci da kuma musulmin Arewa.

TAMBAYA-Shin musulmi ne kaɗai a Arewa? Wannan ya haska masu wannan magana ba Musulmi ba ne don haka ishara na nuna mabiya addinin Kirista ne na Hausa da kuma ‘yan gargajiya da waɗanda mugun nufin ya yi wa zuciyarsu kanta. A ajiye ma batun ishara mu duba yadda Zallawa ke bugin ƙirji cikinsu wai akwai Musulmi, Kirista da gargajiya amma ko sau ɗaya ba mu taba ganin sun karanta Baibul don kafa hujjar Zallanci ba! Ba mu taba ganin sun ɗauko wani kauli na allansu GIJI da giza-gizai da aljana Doguwa don kare hanyar da su ka ɗauka ba.

Gabanin buƙatar INƙAAZ ko wani asusu ya shirya wani taro nan gaba kan darasin da su ka kawo, su biya buki ma na ta hanyar gangami a fadar Sarki Rabaran Shu’aibu Bargi su karanto tanadin da a ka yi wa ƙabilanci a Baibul. Ba ma Bargi kaɗai ba ai kwanan nan na kawo mu ku rukunin kungiyoyin mabiya addinin Kirista na Hausawa da yadda su ke alaƙanta kansu da a na mu su tsangwama. Aƙalla kamar yadda wannan asusu ya gudanar da taro kan illar ƙabilanci a Musulunci da ma bayanan lamuran duniya, su ma su yi irin taron su karanto ruwan hujjoji kan amfani in akwai ko rashin amfanin ƙabilanci a Baibul. Wallahi in su ka yi haka ko ni nan zan kira taro na yi mu su darasin nan da su ka nema. Inda ba kasa a ke gardamar kokawa.

Kusan duk Jumma’a a ɗaruruwan masallatan Arewa a na magana kan matsalar tsaro ko illar ‘yan ta’adda da kuma yin addu’ar neman taimakon Allah. Duk mai inkirari sai mu jefo ma sa fayafayan bidiyo bila-adadin don ya gani idan ya ce bai taba ji ba. Kai ko ma wanda ya yi dabi’ar mutan Annabi Nuhu masu toshe kunnuwa kar su ji wa’azi, za mu sake maimaita ma sa don ya ji hakan ya zama karin yanke hujja karara fayau fal kamar hasken rana da ƙarfe 12pm.

KAMMALAWA

Mu na jiran duk wanda zai karɓi wannan ƙalubale daga Zallawa/mishan ya fito su gudanar da taron don biyan buki. Na ga ko taronsu na baya ba su ja ko aya daya tal daga Baibul ba alhali ga su har sarki su ke da shi. MU NA JIRA!

By ukarofi

Leave a Reply