’Yan bindiga sun harbe Sheikh Yahaya Masussuka a gidansa da ke Dutsin-Ma a Jihar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa da ke garin Dutsin-Ma, Jihar Katsina.

Lamarin ya faru a ƙofar gidan malamin, inda maharan suka buɗe masa wuta tare da wani aminin nasa.

An garzaya da su zuwa babban asibitin Dutsin-Ma domin samun agajin gaggawa, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu ƙarin bayani a hukumance kan wannan mummunar hari da ‘yan bindigan suka kaiwa malamin.

Lamarin ya ƙara jefa al’ummar yankin cikin alhini, musamman mabiyan malamin da waɗanda suka san shi.

By ukarofi

Leave a Reply