Daga ABBA ILIYASU IBRAHIM TSANYAWA
Mawaƙi: Alhaji Dauda Abdullahi Kahutu Rarara
Mai Nazari: Abba Iliyasu Ibrahim Tsanyawa. B.A (BUK)
Gabatarwa:
Waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ da ta ja hankali a Arewacin Najeriya yanzu kuma ta samu shiga fagen nazari, inda wani marubuci kuma mai nazarin adabin baka Abba Iliyasu Ibrahim Tsanyawa ya feɗe waƙar.
Kwarjini da karɓuwa da kuma daɗin waƙar da salonta ake ganin ya ja hankalin mutane musamman matasa (maza da mata) da dattawa da sauran masu sha’awar harkokin adabin Hausa wajen tofa albarkacin bakinsu a kan waƙar, a daidai lokacin da ake cikin yanayin zaman tsadar rayuwa a ƙasar tare da matsalar ƙarancin man fetir, an kalli waƙar a matsayin wata abu da ta rage raɗaɗi tare da farantawa al’umma rai, kamar dai yadda batunta ya karaɗe kafafan sadarwar zamani musamman na Arewacin Nijeriya.
Ana nazarin waƙa ne a fagen ilimi idan ta dace da nazari da kuma abubuwan da nazari yake nema, wannan ne dalilin da ya ja hankalin manazarcin waƙoƙin ganin ya nazarci waƙar ‘Fatima Mai Zogala’, dan kuwa waƙar ta dace da nazari.
Rarara ya saki tallar waƙar ‘Fatima Mai Zogala’ ne a cikin ƙarshen watan huɗu na shekarar 2024, inda ya saki cikakkiyar waƙar a farkon watan biyar na shekarar, kuma sai ga shi ta samu karɓuwa nan da nan musamman a kafafan sadarwar na zamani.
Yadda Manazarcin ya feɗe waƙar:
Waqar ‘Fatima Mai Zogale’ tana da yawan ɗiya aƙalla guda talatin da uku (33). Waƙar ta zama ruwan dare game duniya a tsakanin Hausawa mazauna mabambantan ƙassshen Duniya, da sauran masu sha’awar harkokin Adabin Hausawa.
Alhaji Dauda Kahutu Rarara, ya rera waƙar ‘Fatima Mai Zogale’ ne da harshen Hausa, cikin Karin harshen Kananci, duk da an samu tasirin karin harshen Katsinanci a ciki.
Mutane sun ƙaunaci waƙar wasu domin tausayawa Fatima bisa korarta da uwar daɗinta ta yi, wasu kuma don ganin a karon farko mawaƙin ya yi waƙa ga Talaka (mai sana’a) wasu kuma saboda ƙaunar mawaƙin da kuma kasancewar ba kasafai yake waƙoƙin da ba na siyasa ba, a dan haka aka yi ta hawa waqar, a kwana biyu ta karaɗe Arewacin Nijeriya. Waƙar ta zamo waƙa ta uku a waƙoƙin da ke tashe a Arewacin Nijeriya, daga bisani ta zamo waɗa ta ɗaya kamar yadda binciken masana ya nuna.
Tarihin Mawaƙi:
Alhaji Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, an haife shi ne a Jihar Katsina, a qauyen Kahutu da ke Ƙaramar Hukumar ‘Danja, a ranar 13 ga watan Satumba 1986, shahararren Mawaƙin ‘yan siyasa ne a Nijeriya, mawaƙi a fannin rera waƙoƙi musamman na ‘yan siyasa da sarakuna, kuma mai hasashen abubuwan da ka iya zuwa su zo. Duk da cewa ya taso a garin Kano domin neman ilimin Alqur’ani, ya shiga hidimar waƙa ne aqalla shekaru ashirin da suka gabata. A yanzu a Facebook kaɗai yana da mabiya fiye da miliyan ɗaya, (1,000,000) ga kuma Youtube da Instagram da Ticktock da Tweeter da makamantansu.
Wasu dalilai na amsuwar waƙar:
- Amsuwar Waƙa yana da tasiri da sanuwa ko shura na mawaƙi, kasancewar Alhaji Dauda mawaƙin da furarshi ke kan daho, kuma mai tarin mabiya ya ƙara taimakawa wajen amsuwar waƙar a ƙan ƙanan lokaci.
- Al’umma suna wani yanayi na ƙarancin man fetir, saboda haka zirga zirga ta taƙaita, akwai lokacin sauraren abubuwa, kuma lokaci ne na buƙatar nishaɗi domin rage raɗaɗin matsalar mai da tsadar rayuwa.
- Ba a saba jin Alhaji Dauda yana waƙa ga wani mai ƙaramin ƙarfi ba, sai ga shi a karon farko yana waƙa ga wadda ba tabbacin a same ta da Naira dubu ashirin ta kanta.
- Babban dalili kuma shi ne matakin da uwar ɗakin Fatima ta ɗauka na korarta daga aiki, ya ɗauki hankalin mutane wajen bibiyar al’amarin dan ganin sakamakon da Fatima za ta samu musamman daga wanda ya yi mata waƙar.
2.0 Saƙo ko Tarken Waƙar
2.1 Gundarin Turke
Babban saƙon da wannan waƙa ta ke ƙunshe da shi, shi ne zuga tare da yabawa da kwanzartawa da nuna gamsuwa bisa sana’ar Fatima ta siyar da zogale, kenan jigonta na yabo ne
Mawaqin ya yi ƙoƙari matuƙa wajen fitar da turken waƙar da ma ƙananan tubalai tun daga dan waƙar na farko har zuwa na ƙarshe.
Mawaƙin ya nuna ƙwarewa wajen ƙulla waƙar da ƙafiyoyi na ciki da na waje.
Ya nuna ƙwarewa wajen zaɓo kalmomi zuga da yabo da kwanzartawa a lokacin ƙulla waƙar, wanda hakan ya ƙarama waƙar armashi da daɗi.
2.2 Muhallan Turke na waƙar:
A wasu misalai na muhallan turke na wannan waqa su ne inda ɗa na 7 da ɗa na 5 suke faɗin:
Jagora : na yaba mai zogalan garinnan na gudu ban tsira ba
: Fati masu kwadon zogalanmu rannan tayi murace
: Fati Fatima kenan aradu zancen Fatima bai ɓuya ba
: Kyau da diri naki zan kwatance ba dan ganinki ba
: Kyaykyawa ta fito ku layu
2.3 Taƙaita Turke Waƙar
Saƙonnin da wannan waƙa ta ƙunsa a gunduwa-gunduwa ta ma’ana sun haɗa da:
Ɗa na 1-5: suna wasa wadda ake yiwa waƙa cikin salon na zuga da kambame da yabawa.
Ɗa na 6: bayyana muhallin turken waƙa, wato jigon waƙar.
Ɗa na 7-15 yabo tare da wasu shawarwari ga rayuwar Fatima akan sana’arta da kuma abubuwan da ka iya zuwa su zo.
Ɗa na 16-19 habaici ga maƙiyan Fatima, tare da ƙara tabbatar da asalin Fatima da ƙara mata shawarwarin jan hali da tattali, da kuma rabuwa da maƙiyanta, wato kada ta tanka musu.
Ɗa na 20-22 bayyana wasu siffofin wadda ake wa waƙa, mai ‘yar gira a goshi, mai kwale, tare da shawarwarin ta ƙara riƙe masoyanta hannu biyu, ta kuma yi watsi da maƙiyanta waɗanda ba su ƙaunarta.
Ɗa 23-26 shawarwari ne akan Fatima ta riqe sana’arta hannu bibbiyu, kada ta yarda da bashi kowa ya miƙo kuɗinshi ta ba shi zogale, kowa ya taho siyan zogale ta jira shi, saboda kula da abokan kasuwa.
Ɗa na 27-30 ƙara yaba siffar Fatima musamman kyau da dirinta tare da faɗo wasu kyawawan halayenta irin na taimakon marayu, da ku ma yadda take goya mabuƙata.
Ɗa na 31-33 jaddada yabon Fatima tare da kira a gareta da ta ɗauki shawarwari da bayanan da aka zayyana a waƙe, wato kyan koyarwar ƙwarai a koyu.
3.0 Awon Baka na wannan waƙa:
Yawan layuka na ɗa
Zubin ɗiya a waƙar – An buɗe waƙar ne da kiɗa na kayan kiɗan sitidiyo, wato gangunan Turawa, sannan aka ci gaba kai tsaye da zuba ɗiyan waƙar.
Tsarin ɗa ko ɗiya a waƙar
Tsarin Rerawa
Takidi a ɗiyan waƙar
Karin murya da amsa amon waƙar
4.0 Adonta Harshe a Waƙar:
Alamtarwa = Kalmar Adon gari (ɗa na 24)
Kamantawa = ɗa na 19
Siffantawa = ɗa na 28, da ɗa na 29, da 20: Fatima ga ɗan kwalenta ganshi
5.0 Aiwatar da harshen Waƙa:
Yawan Kalmomin waƙa= waƙar na da kalmomi 605.
Zaɓen Kalmomi = Misali ado, gira, dila, kandala, gudu, labule, ilimi, dangwale, dunƙule, zogale, tsira, bakin uwa, tattali, sangali, marayu, taimako, birni.
Karin Magana: kwalli dai na ido ne: ɗa na 11.
Kyauta ta yi kamar tsintuwa : da na 10.
Karin Harshe na Waƙar = Kananci
Ginin Jumla a Waƙar = Akwai nau’o’i daban-dabam, kamar:
Jumla Sassauƙa: ɗa na 1, ɗa na 17 da 19 da da na 29.
Jumla Tsattsaura: ɗa na 19, ɗa na 11.
Jumla umartau: ɗa na 14, ɗa na 17, ɗa na 18 da na 21.
Jumlar Aikatau: ɗa na 23, ɗa na 24.
6.0 Tasirin Waƙar ga Al’ummar Hausawa:
Waƙar ‘Fatima Mai Zogala’, Waƙa ce da ta fito a lokacin da ake da ƙishirwar wata waƙa irinta wadda za ta samar da farin ciki tare da rage raɗaɗin da al’umma suke ciki. Waƙar ta amsu kuma ta yi tashe, mutane sun amshi waƙar ka in da na in, inda suka yi ta hawanta a kafafen sada zumunta musamman kafar TikTok da Facebook.
Waƙar ta dace da sharuɗɗan da masana suka gindaya na nazarin waƙar baka Bahaushiya, kuma ta dace da kyawawan al’adun Hausawa, ba ta saɓa da koyarwar addinin Musulunci ba, dan kuwa a nazarinta da aka yi ba a samu munana ko ɓatanci ga al’ada da addini ba, ba a samu maganganun tayar da sha’awa ko batsa a cikinta ba, sai ma ƙoƙarin taskace al’adu da tsofaffin kalmomi a cikinta. Dan haka waƙar ba ballagaza ba ce, waƙa ce da za a ƙarfafi mutane da su saurara kuma su nazarta.
Ɓangaren sana’a kuwa, waƙar ta qara fito da mutuncin sana’ar Hausawa ko ace abincin Hausawa wato zogale, dan kuwa wasu alƙaluman bincike sun nuna yadda al’umma suka ƙara qƙaunatar zogalen.
Abba Iliyasu Ibrahim Tsanyawa, B.A (BUK).
Marubuci, Mai sha’awar harkokin Adabi da al’adun Hausawa.
08037672040 Email: [email protected].
