Yawancin matan sojoji sun dogaro kacokam kan abinda mazajensu ke ba su – Rashida Usman Yahaya

“Yaran sojoji suna samun tarbiyya sosai”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ba kasafai ake jin labarin irin rayuwa da gwagwarmayar da matan sojoji da sauran jami’an tsaro masu ɗamara suke gudanarwa a ɓangaren taimakon al’umma da cigaban muhallin da suke rayuwa a ciki ba. Saboda ƙa’idoji da dokokin rayuwar bariki. Amma a yanzu abubuwa sun fara canzawa, wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya samu kutsawa har cikin barikin sojoji na Rukuba da ke Jos, inda ya samu ganawa da Hajiya Rashida Usman Yahaya, wata jajiryacciyar mata mai himma, wacce musamman ta kafa wata gidauniya don ganin ta inganta rayuwar matan sojoji da yaransu da ke rayuwa a cikin bariki. Hajiya Rashida ta kuma bayyana masa burinta na ganin matan sojoji sun samu sana’o’in dogaro da kai, don su iya riqe kansu da taimakawa mazajensu wajen kula da tarbiyyar iyalinsu. Ga yadda hirar tasu ta kasance.

MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanki?

HAJIYA RASHIDA: Salamu alaikum. Cikakken sunana Rashida Usman Yahaya. Shugabar Gidauniyar Tallafawa Mata da Mabuƙata ta Rasheeda Women Foundation. Har wa yau kuma ni ce nake jagorantar ƙungiyar haɗin gwiwar matan Bassa ta Bassa Women for Peace and Unity Initiative, a nan Ƙaramar Hukumar Bassa, da ke Jihar Filato.

Bayan ayyukan ƙungiyoyin al’umma na zaman lafiya da cigaban mata, me kuma ki ke yi na zaman rayuwa?

Akwai ayyuka daban-daban da nake yi, ciki har da shirya tarukan wayar da kai, da na ƙara wa juna sani wanda nake yi wa matasa, don kawar da tunaninsu daga shaye-shaye, bangar siyasa, da faɗace-faɗace irin na sara-suka. Sannan harwayau ina koyawa mata da marasa ƙarfi sana’o’in dogaro da kai, don hana zaman banza.

Ko za ki gaya mana wani abu daga tarihin rayuwarki?

To, kamar dai yadda na faɗa a baya sunana Rashida Usman Yahaya. Ni haifafiyar garin Jos ce a Unguwar Algadama da ke yankin Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Mahaifina asalinsa ɗan Bauci ne, mahaifiyata kuma Ba’angashiya ce daga Ƙaramar Hukumar Pankshin. Na yi karatuna na firamare a makarantar firamare ta Kabong a Gada Biyu, sannan bayan na kammala, na je na yi karatun sakandire a Makarantar Gwamnati ta GSS Pankshin. Bayan na kammala kuma na yi aure, inda na auri mijina wanda soja ne. Ina da yara huɗu, biyu maza biyu mata. Muna zaune a Barikin Sojoji na Rukuba, da ke yankin Ƙaramar Hukumar Bassa.

Mene ne ya qarfafa miki gwiwa ki ka shiga waɗannan ayyuka na taimakawa mabuƙata?

Yanayin halin da muka samu kai a ciki na taɓarɓarewar zamantakewa da rashin zaman lafiya, shi ne ya fara sa ni tunanin yin wani abu don ba da gudunmawa, domin ganin an samu dawowar zaman lafiya da taimakon juna.

Lokacin da muke tasowa mun ga yadda iyayenmu da ƴan uwanmu suka rayu tare da waɗanda ba Musulmi ba a zamantakewar cikin gida, a tsakanin iyali, da kuma a maƙwaftaka. Wasu ma mun zama kamar ƴan uwa ne na jini ɗaya. Amma tun bayan da aka samu rikice-rikice na ƙabilanci da addini a Jos da kewaye, musamman a nan yankin Bassa, na ga ya kamata mu yi wani abu, a dawo da zaman tare irin na da. Don haka na yi ta bibiyar mutanen da na sani da wakilan al’umma daga ƙabilu daban-daban, muka haɗu muka fara gangamin wayar da kai, da tarukan zaman lafiya.

Wanne irin goyon baya ki ke samu daga kwamandojin wannan bariki, kasancewar mun san rayuwar soja tana da tsari da ƙa’idoji?

Na gaya maka mijina soja ne, kuma muna ganin ƙoƙarin da jami’an tsaro suke yi wajen samar da zaman lafiya. Wannan na daga cikin dalilan da suka zaburar da ni ga waɗannan ayyukan. Kuma Alhamdulillahi maigidana da manyan su da ke nan bariki suna ba ni goyon baya sosai a kan wannan aiki da nake gudanarwa. Duk wata ƙa’ida ko doka da muke da su a nan, na bi su daki-daki, don haka ba ni da wata matsala da su.

Me ya ja hankalinki ki ka kafa Gidauniyar Tallafawa Mata da Mabuƙata ta Rasheeda Women Foundation?

A gaskiya na lura da irin halin da mata ke ciki, musamman matan mu na bariki, waɗanda ke fuskantar qalubalen rashin sana’o’in dogaro da kai. Yawancin mu mun dogara ne kacokam ga abin da mazajen mu ke samu na albashi, wanda kuma ba isar mu yake yi ba. Wasu kuma an tura mazajen su zuwa wuraren yaƙi ko aikin samar da zaman lafiya, ba su san yaushe za su dawo ba, ko kuma babu wani ƙwaƙƙwaran mai taimako. Wasu kuma idan mazajen su suka rasu a wajen yaƙi, ba su da wata madogara da suka riƙe, suna shiga matsaloli da dama su da yaransu.

Don haka na kafa wannan gidauniya domin ganin na taimaki mata ƴan uwana da sana’o’in da za su taimake su wajen riƙe gida da kula da iyalinsu. A tashin farko mun horar da matan soja ɗari da hamsin kan sana’o’i daban-daban. Da azumin Ramadan ma an horar da mata ɗari uku, ninkin abin da muka yi na farko, kan abubuwan da suka shafi girke-girke da soye-soye. Kuma in sha Allahu nan gaba akwai shirin da muke da shi na koyar da yaran sojoji, musamman matasa maza da maƙwaftanmu na cikin Bassa su ɗari da ashirin, kan dabarun sana’o’i da nisantar halayen banza irin su shaye-shaye da faɗace-faɗace.

Bayan kun yi musu irin wannan horo na sana’o’i da ki ka ce kuna yi, akwai wani tallafi da ku ke basu ne, kamar jarin fara sana’a, da kayan aiki?

To, gaskiya a nan ne nake samun damuwa, domin kuwa ka san wannan gidauniya zaman kanta take yi. Ba ƙungiya ce ta gwamnati ko ta Babban Kwamandan bariki ba, kuma babu wanda ya ke bani kuɗi daga wani waje. Ni ce na kafa ta bisa raɗin kaina, don haka duk abin da na yi daga asusuna ne. Shi ya sa ba ma iya ba su jari ko tallafin kayan aiki, a halin yanzu, amma nan gaba in damar hakan ta samu, ba abin da zai hana mu tallafa musu. Ina kuma amfani da wannan dama in kira ga shugabanninmu da masu hannu da shuni, su dubi ƙoƙarin da muke yi su tallafa mana, ko da wajen ɗaukar nauyin horon da muke bai wa waɗannan mata da matasa ne, ko kuma ba su tallafin jari da abin fara sana’a a lokacin yayen da ake musu. Ni ko ba su ba ni taimakon ta hannuna ba, su zo su bai wa matan a hannunsu, zan ji daɗi sosai, su ma kuma za su ji daɗi.

Mutane na kallon rayuwar bariki a matsayin wata irin rayuwa ta daban, yaya ki ka samu kanki a cikin wannan bariki bayan da ki ka yi aure?

E, gaskiya ne. A farko na fuskanci kaina cikin wata irin rayuwa da ban saba ba. Amma kuma sannu a hankali har ni ma na koyi yadda ake rayuwa a bariki, wacce rayuwa ce tamkar ta iyali guda, kowa ya san kowa. Kuma duk abin da ya faru na farinciki ko na baƙinciki muna haɗuwa mu taya juna murna ko akasin haka.

Wanne sauyi ki ke ganin rayuwarki za ta kawo wa sauran matan bariki?

Kamar yadda na faɗa a baya, na lura da yadda wasu matan bariki ke rayuwa ta kara zube, babu aiki babu sana’a. Duk da yadda mazajenmu sojoji ke ƙoƙari kan sauke nauyin iyali da ke kansu, za su ji daɗi idan matansu su ma suna tallafa musu. Don haka nake amfani da wannan dama ta gidauniyar da na kafa, don mu gudu tare mu tsira tare. Mu taimakawa rayuwarmu da ta iyalinmu. Kuma in sha Allahu na fara kenan, zan cigaba har sai iya inda ƙarfina ya ƙare. Ina fatan waɗanda ake koyawa waɗannan sana’o’i sun samu abin yi ko da a ɗakunansu ne ko a cikin bariki, su ma suna samun wani ɗan kuɗin shiga.

Wacce gudunmawa mata a bariki za su bai wa mazajensu sojoji don kawo wa rayuwarsu cigaba?

Wannan dama shi ne manufarmu. Mu bai wa mata horo, don su taimaki mazajensu wajen kula da ɗawainiyar iyali. A lokacin da mazajenmu ke bakin daga suna yaƙi don samar da tsaro da zaman lafiya, mu kuma a bariki mu zama masu iya riƙe kanmu, da tarbiyyar ƴaƴanmu, muna taya su da addu’a, har su samu nasara a ayyukan da suke yi na kare ƙasa. Yadda mazajenmu za su yi alfahari da mu, idan sun dawo sun samu iyalinsu cikin tsari da kyakkyawan yanayi.

Yaya alaƙarki da ƙungiyar matan manyan jami’an soji ta NAOWA?

Akwai girmamawa sosai a tsakanin mu, amma babu wata yarjejeniya ta taimakawa juna. Sai dai ina da burin ganin mun tafi tare da su wajen ƙoƙarin ganin mun taimakawa rayuwar matan sojoji da ke rayuwa a wannan bariki. Ina fatan za su ga irin abin da muke yi don su ma su shigo su tallafa mana, ta hanyar ɗaukar nauyin horon koyar da sana’o’i da muke yi. Muna ganin irin nasu ƙoƙarin, amma kuma an ce hannu ɗaya ba ya tafi.

Da ki ka yi maganar tarbiyya sai ta tuna min da hasashen da wasu mutane ke yi kan rayuwar yaran bariki, ana ganin duk wani yaro da ya taso a bariki mace ko namiji ba shi da cikakkiyar tarbiyya, shin haka ne?

Gaskiya ba haka ba ne. Bai kamata mutane su riƙa mantawa da cewa, kowanne ɗa iyaye ne suka haife shi kuma suna son sa. Babu wata uwa ko uba da zai zuba ido ya ga ɗansa ko ƴarsa na lalacewa bai yi wani abu a kai ba. Kamar yadda iyayenmu suka ba mu tarbiyya mu a bariki muna ƙoƙarin ganin namu ƴaƴan suna samu ilimi da tarbiyya mai kyau. Zan iya bugun ƙirji in gaya maka cewa, duk kukan da ake yi kan rayuwar bariki, yaran sojoji da dama sun fi wasu yaran cikin gari tarbiyya.

Ba ma barin yaranmu sakaka, basa cuɗanya da kangararrun yara irin na cikin gari masu shaye-shaye da ɗaukar makami suna faɗace-faɗace. Yaran soja suna karatu sosai a ɓangaren addini da boko, muna da makarantun Islamiyya da hafizai da ke koyar da haddar Alƙur’ani da sauran ilimomi na ibada.

A ƙarshe, mene ne burinki na rayuwa?

Burina shi ne in ga an samu haɗin kai da zaman lafiya, a tsakanin Musulmi da Kirista. Ina fatan in ga matan sojoji sun samu sana’o’in dogaro da kai. Ina fatan ganin wannan ƙoƙari da nake yi ya canza rayuwar wasu.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

In ka ga wane ba banza ba! Sai mutum ya jajirce sannan yake zama wani.

Masha Allah. Na gode.

Ni ma ina godiya ƙwarai da gaske.