Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ministar Harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta kai ƙarar Babban Sufeto Janar ’Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, tare da neman kotu ta dakatar da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji daga aurar ’yan mata marayu 100 a yankin jihar.
Amma kakakin ya caccaki ministar saboda “ta wuce gona da iri,” yayin da ya sanar da cewa an soke bikin da aka shirya.
Matakin da Kennedy-Ohanenye ta bayyana a wani taron ƙara wa juna sani da aka yi a Abuja, wani martani ne ga sanarwar da Sarkindaji ya yi a baya-bayan nan na cewa za a ɗaura auren ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Mairiga da ke karkashin mazavarsa.
A cewar shugaban majalisar, auren marayu zai kasance cikin aikin mazavarsa ga al’ummar Mairiga a ranar 24 ga watan Mayun 2024. Ya yi alƙawarin biyan kuɗin sadaki tare da sayo kayayyakin da suka dace domin bikin ɗaurin auren ga masu ’yan mata masu sha’awar aure.
Da take nuna rashin amincewa da batun kakakin majalisar, ministar ta ce: “Ina so in sanar da kakakin majalisar cewa wannan abu ne da ministar harkokin mata da gwamnati ba za su amince da shi ba. Wajibi ne a yi la’akari da waɗannan yara da makomarsu.”
Da take bayyana rashin jin daɗin ta game da matakin da kakakin majalisar ya ɗauka, ta ce gwamnatin tarayya ta garzaya kotu domin hana irin wannan matakin kuma za ta tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.
“Na je kotu. Na rubuta masa (kakaki) takarda kuma na kai ƙarar IGP. Har ila yau, na ba da umarnin dakatar da shi daga duk wani abu da yake shirin yi a ranar 24 ga watan Mayu, har sai an yi cikakken bincike a kan waɗannan ’yan matan don gano ko sun bayar da izininsu, shekarun su da kuma mutanen da ke neman auren su,” inji ta.
Ministar ta ce an fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin don fahimtar abin da ya haifar da irin wannan batun.
Kennedy-Ohanenye: “Kamar yadda mai magana da yawun bai yi tunanin ba waɗannan mata damar ba, tura su makaranta, ba su wani irin horo ko tallafin kudi, ma’aikatar harkokin mata ta yanke shawarar ɗaukar hakan kuma za mu ilmantar da yaran.
“Waɗanda ba sa son zuwa makaranta, za mu horar da su sana’o’i, mu ba su da kayan aiki masu ɗorewa don ba su damar gina rayuwarsu da yanke shawarar wa da lokacin da za su yi aure.”
A cewarta, idan bisa ga kowane dalili shugaban majalisar ya yi yunƙurin yin sabanin hakan, to za a yi mugun faxa tsakaninsa da ma’aikatar.
Kakakin majalisar a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya, ya ce ba zai halarci daurin auren ba, ya kuma buƙaci ministan da ya ɗauki nauyin bikin.
Ya qara da cewa ba za a cire kuɗaɗen da tuni ya baiwa iyayen ‘yan matan ta hannun shugabannin gargajiya da malaman mazaɓar sa ba.
Sarkindaji ya ce halin talauci da iyayen ‘yan matan ke ciki ne ya sanya shi ɗaukar nauyi ɗaurin auren, amma ba aikin mazaɓu ba, kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka ruwaito.
