Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Kuɗi da Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa, EFCC, ta sake jaddada aniyarta ta gudanar da cikakken bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa Ƙaramin Ministan tsaro, Bello Matawalle, a lokacin da ya ke Gwamnan Jihar Zamfara.
Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata, yayin wani taro a hedikwatar EFCC da ke Abuja tare da mambobin ƙungiyar siyasa ta Tinubu Youth and Women Network, da ke fafutukar gudanar da bincike kan zargin almundahana da Matawalle.
Ana tuhumar Matawalle bisa zargin karkatar da dukiyar al’umma a lokacin da yake Gwamnan Jihar Zamfara daga 2019 zuwa 2023.
A watan Mayun 2023, Hukumar EFCC ta bayyana cewa tana binciken Matawalle kan zargin cin hanci da rashawa, bayar da kwangiloli na bogi, da karkatar da sama da Naira biliyan 70. biliyan.
Ƙungiyar Matasa da Mata ta Tinubu, wadda ke ikirarin haɗa kai da gwamnati wajen magance cin hanci da rashawa, ta matsawa hukumar EFCC lamba da ta gaggauta gudanar da bincike kan zargin almundahanar Matawalle.
Ƙungiyar dai na ɗauke da kwalaye da rubuce-rubuce irin su “EFCC, me ya sa Matawalle ke yawo cikin ’yanci? da “EFCC, shin Matawalle ya fi ƙarfin doka ne? Sun zargi tsohon gwamnan da karkatar da biliyoyin nairori da aka ware domin gudanar da ayyuka a Jihar Zamfara inda suka buƙaci a gurfanar da shi a gaban kotu.
Kwamred Aliyu Yunusa, shugaban qungiyar, ya buƙaci hukumar EFCC da ta sake buɗe bincike kan zargin almundahanar Matawalle.
Ya ci gaba da cewa, “Muna kira ga hukumar EFCC da ta ci gaba da binciken Bello Mohammed Matawalle bisa zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara da kuma hannu a badaƙalar cinikin makamai. A matsayinmu na masu biyayya ga jam’iyya, muna son a tabbatar da adalci don hana wasu shiga ayyukan rashawa.”
A martaninsa, Oyewale ya tabbatar da cewa EFCC za ta isar da saqon su ga shugaban hukumar, Ola Olukoyede, tare da tabbatar da an tafiyar da lamarin yadda ya kamata.
Ya jaddada cewa dole ne a yi cikakken bincike dalla-dalla, yana mai cewa, “Bincike dangane da aikin yaƙi da cin hanci da rashawa, ba abu ne da za a cikin gaggawa ba. Dole ne ya kasance daki-daki, dalla-dalla, da cikakken haɗin kai. Za mu yi abin da ya kamata mu yi. “
A yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, ‘yan Nijeriya na dakon sakamakon binciken da hukumar EFCC ke yi na cin hanci da rashawa a Matawalle.
Tabbacin da EFCC ta yi cewa za ta yi adalci, ba cikin gaggawa ba, ya sanya fatan za a yi adalci kuma waɗanda aka samu da laifi za su fuskanci cikakken ƙarfin doka.
