Batun samar da ’yan sandan jihohi a Nijeriya

Ƙirƙirar ‘yan sandan jihohi dai ta kasance batun da ya daɗe ana muhawara a kai a Nijeriya.

A ranar Litinin ne Majalisar Wakilan Nijeriya ta gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan maganar samar da ’yan sandan jihohi a faɗin ƙasar.

An jima ana tafka muhawara kan batun samar da ’yan sandan jihohi a Nijeriya, sai dai a wannan karon majalisar ta fito ƙarara domin sanya zancen a bainar jama’a.

Masu ruwa da tsaki da dama ne suka halarci taron a ranaf Litinin, ciki har da wasu tsofaffin shugabannin qasar da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya da sauran su.

Amma Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya Kayode Egbetokun ya ce ƙasar ba ta kai ga kafa rundunar ’yan sandan jiha ba duk da ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wani taron tattaunawa game da kafa rundunar ’yan sandan jiha da aka gudanar a Abuja, babban birnin ƙasar da aka yi wa taken “Hanyoyin samun zaman lafiya: Sake fasalin ’yan sanda a Nijeriya”.

Egbetokun ya ce har yanzu Nijeriya ba ta kai lokacin da za ta kafa rundunar ’yan sandan jihohi ba, inji shi wanda ya samu wakilcin AIG Ben Okolo a taron da kakakin majalisar wakilan Nijeriya, Tajuddeen Abbas ya shirya.

Ya ce akwai yiwuwar wuce gona da iri daga gwamnatocin jihohi.

“Gwamnonin jihohi na iya amfani da ’yan sandan domin buƙatarsu ta siyasa ko ta ƙashin kai tare da murƙushe haƙƙoƙin bil adama da tsaro.”

Sai dai ya bayar da shawarwari na yadda za a inganta ayyukan ’yan sanda wajen haɓaka tsaro a ƙasar.

A cewarsa, akwai buƙatar a ƙara yawan jami’an tsaron da ake ɗauka aiki duk shekara. Da kuma ba su horo, abin da ya ce na da muhimmanci wajen tabbatar da tsaro a Nijeriya.

A taron da ya samu halartar manyan jami’ai a Nijeriya, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan yana ganin duk da ƙalubalen da ake fuskanta, kafa rundunar ’yan sandan jihohi a Nijeriya abu ne na dole.

Ya ce ƙaruwar sace-sacen mutane da sauran laifuka ya sa kafa rundunar ’yan sandan jihohi ya zama wajibi a halin da ake ciki a Nijeriya.

A watanni baya dai, ƙudurin samar da ‘yan sandan jihohi a Nijeriya ya tsalake karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai domin shawo kan matsalolin rashin tsaro da suka addabi ƙasar.

Ƙudirin wanda ‘yan majalisar 13 suka ɗauki gabatar, ya samu goyon bayan mafi rinjayen ‘yan majalisar waɗanda suka yi imanin cewa gwamnonin jihohi ya kamata su mayar da hankalinsu ga halin da ake ciki na rashin tsaro a faɗin ƙasar.

Da alamu dai an kama hanyar kawo ƙarshen tirje-tirje da ma tayar da jijiyar wuya a kan wannan batu da aka kwashe lokaci mai tsawo ana ja-in-ja a kan halaccinsa ko akasin haka.

Sakamakon matsalar tsaro da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan, gwamnonin jihohin Arewa 19 ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) da kuma Ƙungiyar Sarakunan Gargajiya ta Arewa (NTRC) sun yi kira da a kafa ’yan sandan jihohi. Gwamnonin da sarakuna sun bayyana cewa, ’yan sandan jihohi za su taka rawar gani wajen magance matsalolin tsaro a yankin Arewa da sauran sassan ƙasar nan. Baya ga haka, babu shakka a halin yanzu ƙasar na fama da matsalar ’yan bindiga, tada ƙayar baya, garkuwa da mutane da sauran nau’o’in laifuka.

Dangane da ƙaruwar rashin tsaro da aikata laifuka a dukkan sassan qasar nan, an cigaba da gudanar da zanga-zangar neman kafa sabuwar hanya kan ‘yan sandan Nijeriya. Magoya bayan kafa ’yan sandan jihohi na ganin hakan zai rage yawaitar rashin tsaro a ƙasar.

Sun kuma yi nuni da cewa tsarin ’yan sanda na tsakiya na yanzu ba zai iya ba kuma ba zai magance matsalar rashin tsaro a tarayyar Nijeriya ba. Sun yi ta rarrashin cewa abu ne mai wuya tsarin ’yan sandan da ake da shi a halin yanzu ya yi aiki yadda ya kamata a ce ƙasa mai girman Nijeriya daga Abuja. Ga alama gazawar tsarin ‘yan sandan ƙasa abu ne wanda ba za a iya ɓoyewa ba. Wataƙila wannan shi ne dalilin da ya sa kira ga ‘yan sandan jihohi ke ƙaruwa tare da samun sabbin kiraye-kiraye a faɗin ƙasar.

Wani ɓangare na shawarwarin taron ƙasa na 2014 shi ne samar da ’yan sandan jihohi. An dai yi ittifaƙin cewa aikin ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen rage yawan aikata laifuka a ƙasar. Tunda kowane laifi na gida ne, samar da tsarin ’yan sanda na jiha, zai daƙile rashin tsaro, idan an sarrafa shi da isassun kayan aiki. Kasancewa kusa da jama’a, jami’an ‘yan sandan jihohi su na da damar sanin kowa da kowa. A lokaci guda, hakan zai amsa ga kiran gaggawa ga al’amuran tsaro.

Tare da isassun matakan bincike na hukumomi, za a kafa ’yan sandan jihohi yadda ya kamata. Hatta tsarin ’yan sanda na yanzu ba za a iya cewa ba lalle ya haɗa kafaɗa da wannan sabon tsarin ba. Idan aka yi la’akari da gazawar da ke tattare da tsarin ‘yan sanda na zamani, lokaci ya yi da za a ba ‘yan sandan jihohi dama. Ma’ana, Nijeriya za a iya cewa ta isa ga jahohi da sauran sassan ’an sanda.

Muna goyon bayan aikin ’yan sanda na jiha da sauran matakan ’yan sanda a ƙananan hukumomi da ma matakan al’umma. Wataƙila wannan ita ce hanya mafi dacewa don tunkarar dodo na rashin tsaro a faɗin ƙasar nan.

A shekarar 2012, a matsayin hanyar tinkarar ƙalubalen tsaron ƙasar, gwamnonin jihohi 36 sun yi kira da a kafa ’yan sandan jihohi. Mun yi imanin cewa gwamnoni za su iya yin aiki tare don tabbatar da cewa an kafa ‘yan sandan jihohi. Kafa ƙungiyoyin tsaro a yankin, irin su Amotekun a Kudu maso Yamma da Ebube-Agu a Kudu maso Gabas yana ƙara jaddada muhimmancin aikin ’yan sandan jihohi.

Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tsaya ƙam ga buƙatar kafa ’yan sandan jihohi ta kuma ba ta kulawa cikin gaggawa.

Muna kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da Majalisar Dokoki ta Jihohi da su gabatar da muhimman dokokin da za su kai ga kafa rundunar ’yan sandan jihohi. Ajanda ce da ba za a iya ɗage ta ba.