Ruwan sama da ’yan bindiga sun ruɗa Neja

*Jama’a na tserewa saboda janye sojoji
*Fursunoni 118 sun tsere daga kurkukun Suleja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jama’a sun yi hijira bayan an rufe sansanin soji da kuma janye sojoji da ke aikin samar da tsaro a ƙauyen Allawa da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Wannan ya zo ne a daidai lokacin da fursunoni guda 118 suka arce daga gidan yarin Suleja sakamakon mamakon ruwan saman da ya rikita gidan kurkukun.

A ranar Alhamis ne sojojin Nijeriya suka rufe sansaninsu bayan bayar sa rahoton yi mu su kisan kiyashi, wanda ya janyo firgici a tsakanin al’ummar yankin da ke fama da hare-haren ’yan bindiga da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da ISWAP.

Allawa dai na ɗaya daga cikin al’ummomin da ke fama da munanan hare-hare ’yan ta’adda a ƙaramar hukumar Shiroro. Mazauna yankin sun ce janye sojojin ya zo musu da mamaki saboda a yanzu haka su da maƙwabtansu na fama da sabbin hare-hare.

Wannan ya sa ɗaruruwansu, mata da tsoffi da ƙananan yara ficewa daga ƙauyen babu shiri, inda suka tasamma tafiyar aƙalla kilomita 50, don neman wuraren fakewa masu aminci.

Mazauna garin sun shaida wa Manhaja cewa sun wayi garin Alhamis ne kwatsam suka ga sojojin na kwashe tantunansu suna shirin barin yankin.

Ɗaya daga cikinsu, da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, janyewar ta zo ne kwanaki biyu bayan motar sojoji ta taka nakiya a kan hanyar Allawa zuwa Pandogari, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da ba a bayyana adadinsu ba.

“A ranar Talata 23 ga watan Afrilun 2024, sojojinmu da ke kan hanyarsu ta zuwa Allawa sun taka bama-bamai da suka yi sanadin mutuwar mutane, wasunsu na kwance a asibiti, lamarin ya faru ne a garin Allawa, akan hanyar Pandogari,” inji shi.

Lamarin na ranar Talata ya zo ne ƙasa da mako guda bayan wasu sojoji shida da wani ɗan banga sun rasa rayukansu a wani harin kwanton ɓauna da ’yan ta’adda suka kai garin Roro.

Wannan ya faru ne a lokacin da ’yan bindiga suke kai hare-hare a garuruwan Roro da Karaga da Rumace da wasu yankuna da ake noma sosai.

Wani mazaunin garin, Malam Yahuza Allawa, ya ce, tun da misalin ƙarfe 4 na asuba wasu da dama suka fice daga ƙauyen, suka nufi Erena, Gwada, wasu kuma sun nufi Kuta ko Zumba domin tsira da rayukansu.

“Wannan babban lamari ne, don Allah a taimaka mana a buga rahoto, yanzu muna kan hanyar barin garinmu, kuma babu isassun babura da motoci da za su fitar da mu cikin gaggawa.

“Muna fata watakila idan kun kai rahoto gwamnati ta kawo motocin da za su kwashe mu zuwa wasu wurare da ke da aminci, kayanmu suna can, ba za mu iya kwashewa ba.

“Wallahi ɗaruruwan ‘yan garinmu sun riga sun bar yankin, ba za mu iya bin hanyar Pandogari ba, saboda babu tsaro, don haka za mu bi ko dai Erena ko ta Gwada ko kuma ta Kuta ko Zumba.

“Daga Allawa zuwa Erena wadda ita ce hanyar da za a iya fita ɗaya tilo. Aƙalla za ta kai kilomita 42, muna takawa ne a kafa saboda babu abin hawa da zai kai mu. Akwai Boko Haram a sauran hanyoyin.”

Ya ce, manoman da ke gudun hijira na da ɗaruruwan awaki da sauran dabbobi a gida, da ma wasu kayayyaki masu daraja da suka haɗa da kayan abinci da suka kasa kwashewa saboda rashin abin hawa.

Ya ce Allawa da al’ummomin da ke makwabtaka da su sun dogara ne da kasancewar sojoji domin kariya, wanda janye su ya zo musu da mamaki.

Yadda fursunoni 118 sun tsere daga kurkukun Suleja bayan mamakon ruwan sama:

Fursunoni kimanin 118 sun tsere bayan ruwan sama ya rusa katangar gidan yarin Suleja da ke Jihar Neja a daren ranar Laraba. 

Jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a lunguna da sakunan garin Suleja da kewaye a yunƙurinsu na kamo waɗanda suka tsere.

An ce fursunonin sun tsere daga gidan yairin ne bayan wata iska mai ƙarfin gaske da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya rushe sashin katangar gidan da suke tsare a ciki.

Wani mazaunin garin, Abdullahi Nura, ya shaida wa wakilinmu cewa fursunonin sun yi galaba a kan jami’an da ke gadi, suka tsere ta hanyoyi daban-daban, inda wasu daga cikinsu suka yi ta jifan jama’ar garin da suka yi yunƙurin tare su.

Abdullahi ya ce, “Jifan da fursunonin ke yi ya lalata wasu motocin da ke ajiye a bakin hanya a cikin garin Suleja.”

Hukumomin tsaro sun ce an kama uku daga cikin fursunonin a cikin daren Laraba a unguwannin da ke kewaye da gidan yarin.

An kuma kama wasu da dama da safiyar Alhamis a Unguwannin Rafin Sanyi da Kwankwaso da ke kan hanyar Suleja zuwa Madalla.

Wakilinmu ya yi ƙoƙarin yin magana da kwamandan ’yan sandan yankin Suleja, ACP Muhammad Sani Musa, amma bai yi nasara ba, domin bai samu wayar jami’in ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto.