American International School ta miƙa wa EFCC N1.1bn wanda Yahaya Bello ya biya wa ‘ya’yansa kuɗin makaranta

Daga BASHIR ISAH

Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta tabbatar da ta karɓi kuɗi $760,000 wanda Abuja American School ta maido a matsayin kuɗin makarantar da tsohon Gwamnan Jihar Kogiya, Yahaya Bello, ya biya wa ‘ya’yansa.

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, shi ne ya bayyana hakan rabar Juma’a a Abuja.

“Makarantar ta maido da $760,000 ga EFCC,” in ji shi

Wannan na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan da makarantar da lamarin ya shafa ta buƙaci EFCC ta ba ta asusun da za ta yi amfani da shi wajen maido da kuɗin da Bello ya miƙa mata a matsayin kuɗin makarantar ‘ya’yansa.

Kafin wannan lokaci, EFCC ta yi zargin tsohon gwamnan ya ciri $720,000 daga asusun gwamnati inda ya biya wa ‘ya’yanss biyar kuɗin makaranta.

A cikin wasiƙar da makarantar ta aike wa ofishin EFCC na shiyyar Legas, ta ce ahalin Bello sun biya $845,852a matsayin kuɗin makarantar ‘ya’yansu “tun a ran 7 ga Satumban 2021.”

Sai dai, makarantar ta ce $760,910 za ta maido, wato bayan ta ware kuɗin karantarwa da sauran hidimar da ta yi wa ‘ya’yan tsohon gwamnan.