An gano matasa 1843 ɗauke da lalurar sikila a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Aƙalla matasa 1843 ne aka gano suna fama da larurar amosanin jini ko kuma sikila a faɗin Jihar Jigawa.

Shugabar ƙungiyar masu fama da sikila ta Jihar Jigawa, zainab Shuaibu Koyawa, ita ce ta bayyana haka a zantawar da ta yi da manema labarai yayin taron bitar da aka shirya wa ‘yan ƙungiyar a tsohuwar sakatariyar Gwamnatin Jihar wanda Kamfanin Global in Medicine Fellowship ya ɗauki nauyin ba da horon.

Zainab ta ce kamfanin na Global zai horar da matasan da suke fama da sikila a ɓangaren zane-zane da calligraphy da kuma yadda ake yin tangran na zamani har ma da koyar da su dabarun rubuce-rubuce littatafan Hausa da Turanci da kuma waƙoƙi.

Ta ƙara da cewa, haka zai sa matasan su riƙa samun kuɗin shiga, kuma zai taimaka musu wajen dogaro da kai tare da saya wa kansu maganguna da suke da buƙata maimakon dogaro da gwamnati akoda yaushe .

A cewarta, maƙasudin bitar shi ne domin a zaƙulo yara masu fasaha da ake da yaƙinin za su iya wasu daga cikin abubuwa da aka faɗa a sama kuma, su ne za su sama wa waɗanda suka yi nasara kasuwa wajen tallata basirarsu a intanet wanda ta haka ne mambobin ƙungiyar suke samun kuɗaɗen shiga a duk inda suke afaɗin duniya.

A hannu guda, Zainab ta koka kan matsalar ƙarancin maganguna a asibiti da ‘ya’yan ƙungiyar suke fuskanta duk da cewar gwamnati tana iyakacin bakin ƙoƙarinta wajen sayen maganguna.