Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kwamitin Matasa kan Tattaunawa da wayar da kan Jama’a, ya buƙaci Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) da ta taimaka wajen kafa ’yan sa-kai ‘Road Marshals’ wanda ya ƙunshi matasa a kowace jiha ta ƙasar nan.
Darakta Janar na kwamitin, Cif Obinna Nwaka ne ya yi wannan roƙo yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa rundunar Corps Marshal Dauda Ali-Biu a ranar Laraba a Abuja.
Ya ce baya ga jawo hankalin matasa domin su zama masu hazaƙa, ƙoƙarin da ake yi zai kai ga samar da hanyoyin da za a samar da tsaro a ƙasar nan.
A cewarsa, ƙungiyar ta yi irin wannan shawara ne a shekarar 2020 amma ba ta samu amsar da ta dace ba.
Nwaka ya ce, an kuma ɗauki wannan matakin ne domin rage zaman kashe wando a tsakanin matasa kamar yadda aka shaida a lokacin zanga-zangar ta EndSars, da kuma samar musu da damar yin aiki a matsayin ƙwararru, tare da haɗin gwiwar kwamitin.
“Idan muka ci gaba da hada kan matasa, akwai wasu ayyuka da za su dauka a kansu. Don haka ne muke wakiltan shirin ‘Road Marshal’ na sa kai don kulawar ku,” inji shi.
Nwaka ya yabawa shugaban rundunar corps bisa vullo da tsare-tsare na jin daɗin ma’aikatan FRSC, yana mai cewa hakan ya kara habaka ayyukan ma’aikatan.
Da yake mayar da martani, Ali-Biu, wanda ya samu wakilcin Comfort Asom, kwamandan runduna ta ayyuka na musamman da hulɗa da ƙasashen waje, ya yabawa ƙungiyar bisa jajircewarsu na cigaban matasa da inganta manufofi da tsare-tsare na gwamnati.
Shugaban rundunar ya bayyana shirye-shiryen tallafawa shirin ‘Road Marshal’ na sa kai da sauran shirye-shiryen sada zumuncin matasa.
