Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano Alhaji Lamin Baba Ɗanbaffa ya bayyana jin daɗinsa akan ƙoƙarin da ƙungiyar koyar da sana’o’i ta Tabarakallah ta ke wajen horar da matasa akan sana’o’i da cusa musu tarbiyya da inganta tsaro.
Ya bayyana haka ne a wajen taron gabatar da ayyuka da ƙungiyar take da kuma yaye waɗanda suka amfana da koyon sana’o’i da aka gudanar filin makarantar Galafima.
Ya ce, duk inda aka ce za a koyawa matasa sana’o’i ba ƙaramin abin alkhairi bane ƙungiya in an kafata akan alkhairi al’umma za su amfana musamman a yanzu da ake gama karatu ba a sami aiki ba aka ce an samar da waje da za a koyar da sana’o’i suna fata Allah ya taimaki ƙungiyar.
Alhaji Lamin Baba Ɗanbaffa Galadanci ya yi alƙawarin zai baiwa ƙungiyar gudunmuwa da ya kamata kuma ba kawai unguwanni takwas da suke a cikinta ba yanzu da yardar Allah sai ta shigo ko ina a jihar domin ganin an kauda yara daga shaye-shaye ta ɗora su akan sana’o’i.
Shima a jawabinsa wakilin fuskar yamma Alhaji Tijjani Sanusi Bayero ya ce taron na ƙoƙarin jawo yara da suke fitine-fitine a jiki domin a ɗora su akan turba ta koyon sana’o’i da mayar da su makaranta.
Alhaji Tijjani Sanusi Bayero ya ce yanzu sun sami nasarar koyawa yara 20 sana’o’i na ɗinki mata da maza su kuma abinda suke fata su cigaba da koyawa saura a cibiyar da aka samar ta Tabarakallah.
Wakilin Fuskar Yamna Alhaji Tijjani Sanusi Bayero ya godewa Hakimin Gwale bisa irin shawarwari da gudunmawa da yake basu domin kyautata cigaban al’umma.
Shima da yake tsokaci a wajen taron Babban jami’in ’yan sanda na Gwale Abdurrahim Adamu ya bayyana jin dadinsa bisa yunƙuri da ƙungiyar Tabarakallah take na ganin ta kyautata tarbiyyar matasa ta koya musu sana’a da za su riƙa yi.
Babban jami’in ’yan sandan na Gwale Abdurrahim Adamu ya ce rashin sana’oi na daga abinda ke tunkuɗa wasu matasan su gurɓace su shiga harkar shaye-shaye da daba. A shirye ’yan sanda suke wajen wajen haɗa kai da al’ummar yankin domin tabbatar da wani tsari na ajiye haɗakar gamayyar jami’an tsaro a filin ofishin na Tabarakallah domin inganta tsaron al’ummar unguwanni.
