Tsaro wani muhimmin al’amari ne da jama’a ke la’akari da shi sosai, musamman a lokacin zaɓe. Sai dai a yau al’amura sun ɗauki wani sabon salo, inda ake samun alƙawurra daga hukumomi a gefe guda, sannan matsalolin tsaro na ci gaba da bayyana a gefe guda.
Duk da haka, ya kamata mu nutsu mu yi nazari cikin hikima. Kada duk lokacin da wani abin takaici ya faru, mu bar fushi ko damuwa su rinjayi tunaninmu. Batun tsaro wani babban al’amari ne da ya shafi kowa da kowa, ba gwamnati ta tarayya ko ta jiha kaɗai ba. Ni da ku muna da rawar takawa ta hanyar sanya ido kan mutanen da muke mu’amala da su, da kuma kula da abubuwan da ke faruwa a unguwanninmu da al’ummominmu.
Haƙiƙa, rasuwar manyan jami’ai irin su Birgediya Janar Rabe Abubakar abin takaici ne matuƙa. Amma bai kamata a mayar da irin waɗannan abubuwa zuwa siyasa ko anfani da su wajen neman wata manufa ta daban ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne neman mafita da hanyoyin da za su taimaka wajen inganta tsaro.
Shawarata ga hukumomi ita ce su ci gaba da kula da amanar da al’umma suka ɗora musu, tare da ƙara azama wajen ɗaukar matakan da za su kawo zaman lafiya da tsaro ga jama’a.
A ɓangarenmu na jama’a kuwa, ya kamata mu zama masu taimakawa jami’an tsaro ta hanyar fallasa masu aikata miyagun laifuka maimakon yawan surutai da zarge-zarge marasa amfani. Haka kuma, wajen ɗaukar ma’aikatan tsaro, ya dace a fifita nagarta, ƙwarewa da cancanta, ba son rai ko son zuciya ba.
Daga MUKHTAR IBRAHIM SAULAWA, Katsina. 07066434519/08080140820.
