Daga ZUWAIRA DAUDA KOLO
MANHAJA: Me ya kamata mace ta yi wa mijinta yayin da ya sanar da ita zai ƙara aure?
Nutsuwa da kauce wa biye wa burin zuciya hakika lokaci ne mafi ƙunci da damuwa kuma a wannan lokacin ana rasa hankali da tunani wanda idan an biye dokin zuciya sai a ga ƙarshe an yi ɓatacciya shi kuma ya yi aurensa. Abu ne da dole za a ga kishi a tare da ita, amma ba irin kishi na cin mutunci, da nuna bai isa ba. A’a kishi dai mai tsafta da zai gane tabbas ta ji ba daɗi, amma da yake abu ne da Ubangiji ya sahale hakan a matsayin halas sai ta danne zuciya. Ta yi haƙuri, ta kuma jira akwai sakamako mai kyau ga masu haƙuri da danniya.
MANHAJA: A wannan hali da muke ciki na matsayin rayuwa, wane kira ki ke da shi ga mata kan haƙuri da mazajensu a ɓangaren hidindimun gida?
Haƙuri abu ne da ya zamo wajibi musamman ga mata sosai idan har ana so a samu fa’ida zaman lafiya.
A tattala abin da miji ya kawo, a kuma ririta wajen ganin an yi abin da ya dace da ɗan abin da za a sarrafa domin ana cikin wani yanayi da dole sai an yi haƙuri komai ya yi tsada, maza suna ƙoƙari da kyar wasu ke iya samowa su kawo gida.
Maza su zamo masu adalci wajen bayar da abin da zai wadatar ko kaɗan ne, kuma idan sun samu canji ko buɗi na bazata su nuna domin hakan zai taimaka lokacin da babu su matan su yi uziri, domin sun fahimci a na yi.
MANHAJA: Wacce shawara za ki ba wa maza magidanta?
Ina kira ga maza da su dubi girman Allah su yi haquri da matayensu, su dinga musu uzuri, su zama masu adalci da kyautatawa iya iyawa, magana mai daɗi. Yaba matayensu idan sun yi girki ko kwalliya, ƙoƙarin kyautata musu da abin da za su iya jin daɗi su sani ana son su.
Kyau ta musamman na kuɗi idan Allah ya hore musu kuma idan chanjin cefane ya yi saura su yafe.
Su girmama matansu su kasance tare su yi hira, su yi walwala su nuna soyayya idan da hali a dinga ɗaukar iyali lokaci zuwa lokaci wajen hutawa.