Za a kashe wa ‘yan majalisun tarayya da na jihohi N724bn a 2024

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Majalisun tarayya da na jihohi 36 a Nijeriya za su kashe kimanin Naira biliyan 724 wajen gudanar da harkokinsu a 2024 da ake ciki.

Bayanai kan yanayin kuɗaɗen da za a kashe wa ‘yan majalisun tarayya da na jihohin a wannan shekarar sun ce, a ɓangare albashi da alawus-alawus kaɗai kimanin Naira biliyan 50 aka ware a kasafin ƙasa.

Sannan biliyan N673.94 wajen sauran harkokin majalisun na tarayya da jihohi da kuma hukumomin da ke ɗamfare da su.

Yayin da za kashe biliyan N8.67 wajen biyan albashi da alawus-alawus na ‘yan majalisa 109 a matakin tarayya, a matakin jihohi kuwa biliyan N24.43 ne za a kashe a kan ‘yan majalisa 360 wajen biyan albashi da alawus-alawus ɗinsu.

Fashin baƙin ya nuna jimillar tsagwaron albashin da Shugaban Majalisar Dattawa zai samu a shekara ya kama miliyan N2.48, yayin da na mataimakinsa ya kama miliyan N2.31m.

A ɓangaren alawus kuwa, Shugaban Majalisar Dattawa zai riƙa karɓar miliyan N33.29, sannan mataimakinsa ya riƙa samun miliyan N30.94.

Sai kuma Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa wanda tsagwaron albashinsa ya tiƙe a miliyan N2.48, mataimakin kuma miliyan N2.29.

Yayin da Shugaban Majalisar zai samu alawus na miliyan N18.33, mataimakinsa kuwa miliyan N17.16m zai samu.

By Editor