Daga BASHIR ISAH
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Babban Bankin Nijeriya (CBN) da ya dakatar da aiwatar da harajin rabin kashi ɗaya (0.5%) na tsaron internet wanda ya tada ƙura a ƙasa, tare da neman a sake nazarin dokar.
Idan ba a manta ba a ranar 6 ga Mayu, CBN ya fitar da sanarwa tare da umuryar bankuna da su ɗabbaƙa sabon haraji na tsaron intanet.
Sabuwar dokar ta nuna za a riƙa biyan kashi 0.5 na hada-hadar kuɗaɗe ta intanet sannan a tattara a zuba a asusun Taaron Intanet ƙarƙashin kulawar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro.
Sai dai da alama dokar ba ta samu karɓuwa ba ga ‘yan ƙasa da ƙungiyar ƙwadago da sauransu.
NLC ta yi watsi da harajin tana mai cewa zai ƙara wa ‘yan ƙasa tsanani rayuwa.
Haka ita ma CPPE ta bakin Daraktanta, Dr Muda Yusuf, ta buƙaci a dakatar da wannan doka.
A nasu ɓangaren, mambobin Majalisar Wakila ta Ƙasa sun umarci CBN ya janye aiwatar da wannan harajin.
‘Yan majalisar sun bayyana matakin a matsayin abu mai sarƙaƙiya.
