Gwamnatin Jigawa ta ware N250m don gyara filin wasannin motsa jiki na Dutse – Eka

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran filin wasnnin motsa jiki na Dutse, hedikwatar jihar Jigawa .

Gyaran fulin ya ƙunshi samar da ƙarin gine-gine irin na zamani da wurin dama da fitilu da dasa ciyawa irin ta zamani domin filin ya yi daidai da filin wasa na zamani da ake yayi a duniya.

Shugaban ƙungiyar wasan ƙwallon kafa na Jihar Jigawa, Alh Sabo Abdullahi Eka, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a filin wasa na Dutse. 

Eka  ya ce tuni gwamnatin Jihar ta ware maƙudan kuɗaɗe da za ta yi amfani da shi wajen yin gyara na wucin gadi a filin wasa na Dutse saboda fara wasan ƙwallon kafa na ƙasa wanda Nigerian Lottery ta ɗauki nauyin shiryawa.

Ana sa ran za a kashe kimanin Naira biliyan ɗaya a ɗaukacin wasanin da suke gudana a halin yanzu a Jihar Jigawa wanda ake sa ran kammalawa ranar Litinin mai zuwa, wasan da aka shafe kusan maki uku da farawa.

Eka ya ƙara da cewa, gwamnati tana gudanar da wasannin ne ba dan cin riba ko samun kuɗin shiga ba, tana yi ne domin ta rage zaman banza a tsakanin matasa, kuma suma su zama masu dogaro da kansu da kuma sama wa matasan aikin yi wanda yin haka yana taimakawa wajen rage yawaitar miyagun aiyuka a tsakanin al’umma .