Editan FirstNews ya aijiye aikinsa bayan tsare shi da sojoji suka yi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Editan FirstNews, Segun Olatunji, ya yi murabus sa’o’i bayan da jaridar ta nemi afuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Olatunji, wanda ya shafe kwanaki 14 a hannun hukumar leƙen asiri ta tsaro (DIA) da ke Abuja domin bayar da rahoto kan Gbajabiamila, ya ce ya yi murabus ne domin kare lafiyarsa da na iyalansa.

Hakan ya faru ne bayan wani rahoto da Olatunji ya rubuta mai taken: “Yadda Gbajabiamila ya yi yunqurin karkatar da dala biliyan 30, gidaje 66 ta hanyar Sabiu”.

Kamfanin FirstNews, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 8 ga Mayu, ta ce ta gano labarin da ke ƙunshe da “ƙarya da labaran da aka raba mana a matsayin gaskiya ta wata majiya wacce ta yi sakaci sosai a ɓangarenmu kuma muka nadamar sakawa inda muke neman uzuri ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.”

Ya fusata da neman afuwar, ya yi fatan gaskiya za ta fito da wuri kan abin da ya faru da shi kan rahoton.

Wasiƙar murabus ɗin nasa ta ce: “Saboda sabon cigaban da aka samu dangane da labarin Gbajabiamila da kuma matsayin Gudanarwar kamfanin, na miƙa takardar murabus ɗina a matsayina na Babban Editan Labarai na FirstNews.

“Ya zama tilas a gare ni in yi murabus daga muƙami na don kare lafiyata da ta iyalina.

“Duk da haka, ina so in bayyana cewa nan da wani lokaci mai nisa, gaskiya za ta fito sannan kuma za a ɗauki maganata a kan nasu.

“Ina fata Hukumar Gudanarwar First Media Network Limited, masu buga jaridar FirstNews, za su yi rawar gani wajen biyan albashin da nake bin su na tsawon shekara guda, nan da wani lokaci.

“Ina godiya ga mahukuntan kamfanin da suka ba ni damar ba da gudunmawa waje gudanarwar da la’amura a kamfanin a cikin shekaru huɗu da suka gabata.”

By Editor