*Yayin da matarsa ta rasa idonta guda
Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, Tijjani Babangida, ya rasa ɗansa Fadil mai kimanin shekara guda da haihuwa a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su.
Haka nan, an ce matarsa Maryam ta rasa idonta ɗaya a sakamakon hatsarin wanda ya auku ranar Alhamis a hanyar Zariya zuwa Kaduna.
Kazalika, wani ɗan uwan mahaifin Tijjanin, mai suna Ibrahim Babangida shi ma ya rasu sakamakon hatsarin.
Har wa yau, bayanai sun ce wani ƙarnin Tijjani mai suna Ibrahim wanda shi ma yake cikin motar, nan take rai ya yi halinsa.
Majiya ta kusa da Tijjani Babangida ta ce, “Wannan mawuyacin lokaci ne ga abokinmu Tijjani da ahalinsa.
“Bayan rasuwar Ibrahim, ɗansa ma ya rasu a asibiti jiya (ranar Juma’a).
“Yanzu haka yana cikin mawuyacin hali sakamakon rasuwar ƙaninsa. Matar ta rasa idonta ɗaya saboda mummunan raunin da ta ji a fuska.
“Tuni an ɗauki Tijjani zuwa wani asibiti a Abuja inda ake yi masa magani na raunukan da ya ji.”
Tijjani shi ne Shugaban Ƙungiyar ‘yan ƙwallon ƙafa ta ƙasa, wato PFAN a taƙaice.
