Manyan jami’an sojin Nijeriya 29 sun yi murabus

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

A ranar Juma’ar da ta gabata wasu Janar-janar na sojin Nijeriya 29 suka yi murabus daga aiki a barikin soji da ke Jaji, Jihar Kaduna.

Majiyarmu ta ce 19 daga cikinsu Manjo-janar ne, yayin da 10 ke da muƙamin Birgediya-Janar.

Daga cikin jami’an da lamarin ya shafa har da Manjo Janar Victor Ezugwu, wanda ya wakilci takwarorinsa wajen yin jawabi.

Da yake jawabin, Victor ya ce yaƙi da ‘yan ta’adda zai zo ƙarshe ne idan aka ƙarfa wa dakaru salon yaƙin dare da sauransu.

Ezugwu ya yi kira ga manya da ƙananan sojojin da ke bakin aiki da su ƙara himma wajen yaƙi da maƙiya.

Haka nan, ya yi kira ga waɗanda za su gaje su da su nuna ƙwazo tare da yi wa ƙasa aiki tuƙuru fiye da wanda su suka yi.

By Editor