Yanzu-yanzun: An kori shugaban jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Tukur Danfulani

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar APC reshen Galadima dake ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara, ta kori shugaban jam’iyya na jihar, Alhaji Tukur Danfulani Maikatako, daga jam’iyyar inda ta ce ba shi da ikon jagorantar jam’iyyar a jihar.

A yayin ganawa da manema labarai ranar Asabar a Gusau, babban birnin jihar, ’yan majalisar zartarwa na jam’iyyar APC dake mazaɓar Galadiman, sun bayyana cewar sun ƙuduri aniyar ceto jam’iyyar daga mummunan shugabancin Alhaji Tukur Danfulani.

Kakaki kuma mataimakin shugaban jam’iyyar APC Gundumar Galadima na ƙaramar hukumar Gusau inda shugaban jam’iyyar na jiha, Alhaji Garba Bello ya bayyana cewa 16 daga cikin 27 na yankin sun sanya hannu kan korar Tukur Danfulani daga jam’iyyar.

“Abin takaici ne yadda ake zargin shugaban jam’iyyar APC na jihar Tukur Danfulani Maikatako da raba kan jam’iyyar saboda mummunan shugabancinsa, wanda ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, kuma yana bayyana tun daga matakin ƙasa zuwa jiha”.

Ya jaddada cewa, “ana kuma zargin Tukur da hannu a wasu batutuwa da suka shafi sha’awa yana ba da muƙamai ga waɗanda ba ‘yan majalisar zartarwa ba ne,” hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu.

“Misali, Tukur Danfulani yakan mayar da al’amuran jam’iyyar zuwa ga waɗanda ba Excos ɗinsa ba, wanda hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar”.

A cewarsa, kashi 90 cikin 100 na mambobin jam’iyyar APC a Galadima ward sun amince tare da sanar da ‘ya’yan jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Gusau da hedikwatar jiha da ta ƙasa cewa an kori Tukur Danfulani Maikatako daga jam’iyyar.

Don haka shugaban jam’iyyar APC na gundumar Galadima, ya buƙaci shugabannin jam’iyyar na ƙasa da su gaggauta tura shugaban riƙo zuwa jihar Zamfara, kasancewar Tukur Danfulani Maikatako ba ɗan APC ba ne.