Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta buƙaci magoya bayanta da su yi watsi da batun dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Hon. Tukur Umar Danfulani.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da aka miƙa wa Blueprint Manhaja a ranar Asabar mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Yusuf Idris, a Gusau.
A cewar sanarwar, dakatarwar da aka yi wa shugaban ya samo asali ne daga wasu ɓata-garin mambobin jam’iyyar da ke nuna kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar a mazaɓar Galadima da ke ƙaramar hukumar Gusau.
“Hedikwatar Jiha, Kwamitin Ayyuka na Jiha da mahukuntan jam’iyyar na Jihar na son bayyanawa a fili cewa, babu ƙamshin gaskiya kan yunƙurin dakatar da Shugaban Jam’iyyar na jiha Alh. Tukur Danfulani.”
“Kuma Jam’iyyar tana sane da irin waɗannan ɓata-gari da wasu ‘yan siyasa da ke shirin ruguza jam’iyyar a shirinsu na neman kafa sabuwar jam’iyyar a zaɓen 2027 da kuma ƙoƙarin haifar da matsala a jam’iyyar APC kamar yadda ake yi a Kano da jihohi da dama. Hakazalika, mun yi imanin mugunyar shirinsu ba zai yi nasara ba,” in ji sanarwar.
Ta ci gaba da cewa, “Ya kamata idan wasu na da ƙorafi dangane da Shugaban Jam’iyyar, akwai hanyoyin da tsarin mulki ya shimfiɗa da kuma ka’idoji na magance irin waɗannan ƙorafe-ƙorafen da ba a bi su ba, don haka, dakatar da Shugaban Jam’iyyar babu ƙamshin gaskiya kuma ba ta da tushe balle makama”.
Jam’iyyar ta bayyana cewar yunƙurin dakatar da Shugaban Jam’iyyar wani shiri ne domin kawo cikas ga haɗin kan da ake samu a tsakanin shugabannin jam’iyyar da mambobinta a dukkan matakai dake faɗin Jihar.
Jam’iyyar ta buƙaci kafofin yaɗa labarai da su guji yaɗa labarai ba tare da tantancewa ba daga hedkwatar jam’iyyar a jihar.
“Duba da takardar da ke ƙunshe da zargin dakatarwar, ba ta da tambarin jam’iyyar APC ko kuma takardar shedar Galadima Ward, wanda hakan ya nuna ƙarara dakatar da Shugaban Jam’iyyar bai tabbata ba.”
Jam’iyyar ta ci gaba da cewa, an samar da duk tsarin da za a binciko waɗanda aka ce sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar domin a samu zaman lafiya, da doka da oda a cikin jam’iyyar