Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin Dr. Zaid Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar tattaara haraji ta jihar Kano (KIRS).
Gwamnan ya kuma amince da naɗin Kassim Ibrahim a matsayin Daraktan zartarwa na hukumar tara kuɗaɗen shiga.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da babban daraktan yaɗa Labarai na gwamnan jihar Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a daren ranar Talata.
Gwamnan ya ce sabon tsarin gudanarwar zai fara aiki nan bada daɗewa ba yayin da tsohon shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga na jihar Kano Alh. Sani Abdulkadir Dambo ya koma aiki a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin zuba jari.
