
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Kebbi ta ce ta kama wani mutum mai suna Bello Abubakar ɗan shekara 45 kuma ɗan ƙauyen Ganwo da ke Ƙaramar Hukumar Yauri ta jihar bisa zargin sa da hannu a yunƙurin kisa da fashi da makami.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Bashir Usman ne ya sanar da haka a wata takarda a Birnin Kebbi, ranar Talata.
A cewar sanarwar, al’amarin ya faru ne a ranar 23 ga Agusta, 2026 da misalin ƙarfe 4 na yamma, inda aka samu wani Bello Umar ɗan shekara 22 mai sana’ar tuƙa adaidaita sahu na ƙauyen Wasagu da ke Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu cikin mummunan rauni a kansa a yankin bayan garin Tungar Dariya kusa da ƙauyen Maƙera a Ƙaramar Hukumar Shangu.
Ganin haka ya sanya aka garzaya da shi zuwa Babban Asibitin Koko, inda aka masa magani kuma aka sallame shi.
Bincike ya nuna cewa, wanda ake zargin ya samu dan adaidaita sahun ne daga garin Koko zuwa Tungar Dariya inda ya farmake shi da fartanya, sannan ya rufe shi da ganyayyaki da tunanin cewa ya rasu, kana ya gudu da adaidaita sahun zuwa garin Yauri.
A yayin binciken bin diddigi ta bayanan sirri, an gano tare da ƙwato adaidaitan da aka sacen, lamarin da ya kai ga cafko wanda ake zargin. Akan haka ne aka miƙa al’amarin ga Cibiyar Binciken Miyagun Laifuka ta jihar (CID) domin gudanar da binciken ƙwaf da kuma gurfanar da wanda ake zargin don ya fuskanci hukuncin doka, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
