
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hedikwatar Tsaro DHQ, ta ce sojoji sun gudanar da atisayen tsaro guda 7,062 a sassan Nijeriya a watannin Yuli da Agusta, inda suka yi nasarar halaka ‘yan ta’adda 1,487 da mayaƙa da kuma ceto wasu mutane 177 da aka yi garkuwa da su.
Daraktan Yaɗa Labaran Hedikwatar Tsaron, Manjo-Janar Samaila Uba ne ya bayyana haka a yayin ganawa da ‘yan jarida a ranar Talata. Ya bayyana cewa, an gudanar da atisayen ne ta ƙasa, sama da kuma ruwa, waɗanda suka mayar da hankali kan magance matsalolin ayyukan ta’addanci, ɓarayin daji, garkuwa, safara makamai, satar ɗanyen mai da wasu miyagun laifuka.
Haka kuma, ya ce sojojin sun kama mutane 354 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci, ƙwato bindigu 91, alburusai 1,331 da kayan ababen fashewa 44 yayin atisaye daban-daban.
A cewarsa, atisayen dakarun sojojin na da nufin karya lagon aikata miyagun laifuka a sassan ƙasar, lalata hanyoyi raba kayan aikin masu aikata laifuka, ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, bai wa ƙauyukan kariya da kuma kare muhimman kadarorin ƙasa.
Manjo-Janar Uba ya ƙara da cewa, sojojin ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙaddamar da hare-hare kan ‘yan ta’adda da ƙoƙarin daƙile barazanar da ake fuskanta a sassan Nijeriya ciki har da ta’addanci, ayyuka ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma kai wa ƙauyuka hare-hare.
Kazalika, ya ce atisayen sun kuma mayar da hankali akan daƙile ayyukan tashin-tashinar ‘yan tawaye, daƙile ayyukan satar ɗanyen mai da tacewa ta haramtattun hanyoyi da kuma katse hanyoyin aikata miyagun laifuka da masu taimaka wa tsare-tsarensu.
Har wa yau, ya bayyana cewa, sojojin sun yi gagarumar nasara a Arewa maso Gabas inda dakarun Atisayen Haɗin Kai suka halaka mayaƙan Boko Haram/ISWAP guda 309 da kama wasu da dama da ke taimaka wa ayyukansu. Sannan, ya ce an ceto ɗaruruwan mutane da aka yi garkuwa da su gami da tilasta wa mayaƙan da iyalansu miƙa wuya a gare su.
